Monday, 17 June 2024

Nagartattun Hanyoyi 5 Na Sace Zuciyar Budurwa Ko Bazawara

Tura Wannan Zuwa Ga

A gaskiya sace zuciyar mace abu ne mai sauƙi ga wanda ya gane sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba.


Hanyoyi 5 Na Sace Zuciyar Budurwa Ko Bazawara
Hoto: Create Vista 


MarubuciAbba Rabi'u Matallawa


Tabbas idan dai har kana so ka yi wa mace satar zuciya dole ne sai ka bi dokoki kamar haka:


1. Jan-Aji: ka sani fa mace ba za ta iya mallaka maka kanta haka nan kawai ba, dole ne sai ta ja maka aji don ta gane halayenka da haƙurinka, sannan kuma za ta so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba, saboda mata sun tsani duk wani saurayin dake shirin yaudararsu, idan har ka ga ka zo wa mace kaitsaye ta amince da kai ba tare da jan aji ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar gogaggiyar mace ce to za ta ja maka aji sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.


2. Haƙuri: Tabbas dole ne sai ka zamo mai haƙuri idan ba haka ba ba za ka samu damar lashe jarabawar da mace za ta yi ma ba saboda za ka ga ababe da dama masu gasa zuciya, idan har ba ka zamo mai haƙuri ba; to kai da yin soyayya da mace sai dai a hankali.


3. Gaskiya: mace ta fi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai-tsaye, idan har kai maƙaryaci ne to ina mai tabbatar ma da cewa idan har ta zo ta gane sirrinka za ka sha kashi, don haka ake kwatanta gaskiya daidai gwargwado.


4. Kulawa: dole ne idan dai har kana son zamanka da mace ya ɗauki tsawon lokaci kuma yasa ta soka sosai fiye da kima to lallai kuwa dole ne sai ka kula da ita tamkar yadda za ka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya. Kulawa yana ɗaya daga cikin siffofin abin da mata suke so.


5. Rarrashi tare da girmamawa: Mace ta fi so idan har ka sanyata yin fushi to ka rarrasheta tamkar yadda za ka rarrashi jaririya.


Kuma mace za ta ji daɗi sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata, ta fannin yabon halayenta na kirki tare da nuna mata cewa babu wadda ka fi so a duniya tamkar ita saboda tana da halin kirki.


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user