Har da kai Brutus !
Lokacin da aka soki Julius Ceaser da wuƙa, wannan sukar tana cikin suka da wuƙar da tarihi yake ganin tana cikin mafi munin suka da wuƙar da aka yi a Tarihin Ɗan Adam. Wannan sukar ita ce sukar da akawa Emperor na Rome "Julius Ceaser" lokacin da a ka yi masa kashin mummuƙe a fadarsa.
Marubuci: Shehul Islami Aminu Bello
Abu ne mai baƙin ciki da takaici lokacin da duka waɗanda Julius Ceaser ya amince da su suka yaudare shi. Lokacin da suka haɗu suka haɗe masa kai domin ganin bayansa, inda suka shiga suna sukarsa da wuƙa ɗaya bayan ɗaya, amma yana tsaye kan dugadugansa bai faɗi ƙasa ba, tare da dukkan wann sukar da su ka yi masa ga jini ta ko'ina uba a jikinsa, har sai da ya ga Abokinsa Amininsa Brutus.
Julius Ceaser yana cikin wannan jinin ya na kallon Amininsa Brutus irin dubin samun fatan kuɓuta daga wannan harin, saboda yaƙininsa cewa Amininsa Brutsu ya zo ne domin ya ƙwace shi daga hannunsu ya kuɓutar da shi, Ceaser ya ɗora hannayensa a kan kafaɗun Amini Brutus domin tsammanin agajinsa, kawai Brutus sai matsowa ya yi kusa da Ceaser sai ya shiga yana daɓa masa Wuƙa yana sukarsa da wuƙa, anan ne Julius Ceaser ya faɗi Maganarsa shahararriya " Yanzu har da kai Brutus" Yanzu kam dole Ceaser ya mutu, sai Ceaser ya faɗi kaitsaye ya mutu.
Wannan sukar ta Brutus ita ce mafi tsananin raɗaɗin dukkan sukar da aka yi masa, saboda Amininsa Brutus ba wai kawai sukarsa ya yi da jikinsa ko zuciyarsa ba, sai dai tsammanin da ya saka a gare shi na samun cetonsa ne yasa baƙin cikin wannan ɓacin ran ya kashe shi, dole ya sallama ya faɗi ya mutu.
Tambayar ita ce : Yanzu Brutus nawa ne muke rayuwa da su muna kyautata musu zato, amma sai zaton mu ya yi tasgaro a kansu?
A yau muna tare da mutanen da muke ɗaukar su a matsayin Aminai, amma mayaudara ne da za su samu dama za su daɓa mana wuka bisa ƙashin zuciya kamar yadda Brustu ya daɓa ma Amininsa Ceaser.
Mafi ban takaici da baƙin ciki, Brutus bai isa da wannan kisan baƙin ciki da ya yi ma amininsa ba, sai da aka zo jana'izar ya tsaya yana jawaban ɓata masa suna gaban talakawan ƙasar, tare da siffanta amininsa da cewa " Mutum ne mai yawan buri".