Monday 22 July 2024

Asalin Shubuha Da Hakikanin Ma'anar Ta Tare Da Manufar Masu Amfani Da Ita

Tura Wannan Zuwa Ga

Ma'anar Shubuha


Shubuha kalma ce ta larabci wacce take nufin makamanci ko kuma abu mai rikitarwa. 


Me ce ce Shubuha?
Hoto: A great dream



MarubuciAhmad Murtala Mansur


Shubuha a yaren masana shari'ar musulunci tana nufin abin da ya yi kama da gaskiya amma ba gaskiya ba ne, wato abin da aka kafa hujja da shi wanda ya yi kama da tabbatacciyar hujja amma ba tabbatacciya ba ce, saboda kasancewar ta ta ƙunshi wani abu na gaskiya da kuma wanda ba na gaskiya ba, ta yadda sai ƙwararrun masana ne suke iya gane hakan.


Wato a zahiri sai ka ga kamar dalili ne mai ƙarfi, amma idan aka warware shi sai ka ga ba dalili ba ne, kura ce kawai lulluɓe da fatar akuya.


Addinin musulunci addini ne mai sauƙin fahimta da aiki da shi ga wanda Allah Ta'ala ya yi wa ni'imar shiriya da kyakkyawar fahimta da tsarkakakkiyar zuciya da kuma lafiyayyen hankali. 


Gaskiya a bayyane take, haka ƙarya ma a fili take , sai dai in mutum ya zaɓawa kan sa bin karkatacciyyar hanya to babu yadda za ka iya da shi, saboda ita shiriya ta Allah ce.


Allah Ta'ala ya bayyana komai na wannan addini a harshen Manzon sa sallalahu alaihi wa sallam a cikin Alƙur'ani mai girma da Hadisan sa masu tsarki. 


Bai bar duniya ba sai da ya bayyana komai filla-filla,  kuma amintatattun almajiran sa wato Sahabbai Radiyallahu anhum ajma'in suka ci gaba da yaɗa wannan addini da koyar da shi bayan komawarsa ga mahaliccinsa. Haka wannan addini ya mamaye duniya kuma zai wanzu har ƙarshen zamani. 


Duk da kasancewar musulunci addini ne da babu wani rikici ko abu mai ɗaure kai a cikin sa ga mai ingantaccen imani da lafiyayyen hankali, amma an samu wasu masu muggan manufofi ga wannan addini da suke ta tayar da ƙura domin ta rufe haske da tsarki da tsafta ta wannan addini.


Burin su shi ne su karkatar da musulmi su kautar da su daga sahihin musuluncin da Manzon Allah sallalalahu alaihi wa sallam ya koyar kamar yadda almajiransa sahabbai da masu bin su suka fahimta zuwa ga ta su fahimtar da ra'ayin.


Domin su ja hankalin mutane sai su ɗauki wani abu na gaskiya su haɗa shi da ƙarerayi,  ko su canja masa fassara su murguɗa shi iya son ran su, kuma su kafe akan cewa haka ake nufi. Kuma su yi ta rigima da duk wanda ya yi yunƙurin ya fahimtar da su gaskiyar al'amari har ma su yi ta jifan sa da ƙazaman kalamai su kuma ɗaura gaba da shi.


In ba ai sa'a ba sai ka ga wata gagarumar fitina ta ɓarke a tsakanin mutane.


Mutane masu ƙarancin ilimi da fahimta , da masu son zuciya sai su ɗauka cewa wannan wani babban ilimi ne alhali kuwa jahilci ne tsantsa. 


Wannan shi ake kira SHUBUHA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user