Friday, 12 July 2024

Hanyoyi 3 Na Tantance Makomar Soyayyar Ku Ga Budurwar Nesa

Tura Wannan Zuwa Ga

Soyayya ba ta mutuwa, sai dai ƙarfin ta na ƙaruwa da ƙaruwar lokaci. (Kodayake akwai waɗanda suke mata kisan gilla).


Hanyoyi 3 Na Tantance Makomar Soyayyar Ku Ga Budurwar Nesa
Hoto: Quora


Marubuci:- Kabir L Shu'aibu Kudan


Duk nisan tazara, ba ta yanke soyayya. 


Wayar salula ta kan kasance tamkar tsani ko takin da ke sadar da mu da masoyan mu ko rayar da soyayyar a cikin zukatan mu.


Zuciyar mu ta kan tsinci kanta cikin taraddadi da kokwanto, game da masoyan mu da suka mana tazara; shin soyayyar su gare mu, ta gaskiya ce?


A nan zan so lissafo wasu alamomin da za su ba ka damar fahimtar soyayyar da masoyiyar ka da ta ke nesa da kai ta ke ma, ta gaskiya ce, ko akasin haka.


1. TANA GOYON BAYAN KA A KOYAUSHE.


Duk da tazarar ƙasa ko tekun da ke tsakanin ku, hakan ba zai hana ta goyon bayan ka ba. 


Idan kana da wata tattaunawa mai muhimmanci, ba za ta dame ka ba ta hanyar yawaita kiranka ba, hakan ke nuni da tana matuƙar goyon bayan ci-gaban ka.


Ta san ba ta buƙatar ta ɗaga hankalin ta a kan wa za ka haɗu da su, ko ka yi sababbin masoya, ba ta maka leƙen asiri, don tabbatar da gaskiyar ka.


2. TANA WARE MAKA LOKACI DAGA CIKIN LOKACIN TA.

 

Tunda muhallin ku daban yake da na juna, hakan zai sanya ku kasance cikin hada-hadar wasu ayyukan rayuwa, wataƙila a yayin da kake ƙoƙarin hutawa, a wannan lokacin take ƙoƙarin kama aiki, ba za ku iya samun daidaiton lokacin hutu ba, amma har idan ta ware wani lokaci na musamman don ta saurare ka, to tabbas soyayyarta ta gaskiya ce.


3. TA YARDA DA KAI.


Akwai jumlar da ta fi "Ina son ka" daɗin saurare, ita ce; "Na yarda da kai". Duk wanda ya yarda da kai, tabbas yana ƙaunar ka, amma ba lallai duk wanda yake ƙaunar ka ya kasance ya yarda da kai ba.


Domin tabbatar da ta yarda da kai; ya kamata ka fara yarda da ita.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user