Wednesday 24 July 2024

Hanyoyi 5 Na Samun Zaman Lafiya A Tsakanin Kabilu

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan kuka nazarci ƙasashe daban-daban da suka ci-gaba a duniya, za ku fahimci cewa duk waɗannan ƙasashe na ɗauke da mutane masu al'adu daban-daban, da ƙabilu, da addinai da abubuwa iri-iri.


Inganta Samun Zaman Lafiya A Tsakanin Kabilu
Hoto: Zikoko


MarubuciBello Galadanchi


Sau da yawa za ku ga cewa mutanen nan daga wasu ƙasashe suka zo, amma duk da haka ana zaune lafiya da su, su ma suna lasar zumar ci-gaba da bunƙasar tattalin arziki da walwala mai inganci. Wannan na ɗaure wa jama’a da yawa a nahiyar Afirka kai, saboda suna mamakin yadda ake samun zaman lafiya da ma ci-gaba. 


Tambayar anan ita ce me ya sa ƙabilu daban-daban a Najeriya suka gagara laƙantar zamantakewa tare? Wannan rubutu zai nuna hanyoyin da za a ji daɗin zama tsakanin ƙabilu, lamarin da zai ka ga gina tattalin arziki mai ƙarfi.


1. INGANTA SADARWA: Wato mafi yawancin zaman doya da manja dake shiga tsakanin al'umma na da nasaba da rashin fahimtar juna. Saboda haka, akwai matuƙar muhimmanci jama’ar ƙabilu daban-daban su fahimci manufofi sosai dangane da tsaro, kiwon lafiya, ilimi da sauran batutuwan yau da kullum. Ya zamanto an bayyana duka waɗannan manufofin a sawwaƙe yadda kowa zai gane, ya kuma iya bayyana wa kowa yadda za a fahimta. 


2. ADALCI: Dole sai mutum ya san nauyin dake kansa, kuma an kiyaye nuna bambanci. Idan kuwa ba a yi haka ba, to wariya za ta shigo tsakani inda al'umma za ta rabu tsakanin “mu” da “su”.

 

3. WAKE DA SHINKAFA: Ka yawaita buɗe mu’amala, ayyuka, sana’o’i, tattaunawa da duk wasu hulɗoɗin rayuwa ga kowa, ba tare da nuna bambanci ba. Wannan zai sa a ringa kimanta kowa bisa hali da ɗabi’u, ba yadda al'umma take kallon ƙabilar sa ba ko ƙyamar ta. 


4. KOWANE ADDINI NA DA NASA HALAL DA HARAM: Kar ka mayar da hankali a kan addinin ka kai kaɗai. Duk wani addini na da nasa sharruɗan. Ka fahimci hakan, sannan ka yi ƙoƙarin ganin ka girmama waɗannan sharruɗa. Duk wanda ka yi wa hakan, zai girmama ka, sannan zai girmama addinin ka, ko ƙabilar ka.


5. KA GIRMAMA BUKUKUWAN WASU ƘABILUN DA AL'ADUN SU: Ka aikawa abokan aikin ka, ko maƙotan ka, ko ‘yan makarantar ku saƙon taya murna, ko nuna haɗin kai a lokacin da suke bukukuwan al'adun su ko addinin su, ko kuma suke fama da wata matsala. Wannan yana ƙara zumunci da zamantakewa mai inganci. Idan ka yi musu, su mu za su yi maka.


A ƙarshe, shugabanni su ne iyayen al'umma. Jama’a na lura da su, sannan su na koyi da su. Dole sai sun taka rawar gani sosai wajen inganta zamantakewar ƙabilu daban-daban sannan jama’a za su kwaikwaya. A guji duk wani shugaba mai raba kan jama’a. Allah Ya ɗaukaka mana ƙasar mu ta gado.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user