Sunday, 28 July 2024

Hanyoyi 6 Na Zama Attajiri A Sana'ar Abinci

Tura Wannan Zuwa Ga

Babu shakka a halin yanzu ana fama da rashin kuɗaɗen fara sana’a, musamman idan ana buƙatar shago da kayan aiki. Babu komai, ka fara a gidanku domin ɗaukar darussa, sannan idan ka samu karɓuwa, kuma mutane suka fara jin daɗin yadda kake gabatar da sana’arka, to sai ka tara ribar ka, ka buɗe shago.


Zama Attajiri A Sana'ar Abinci
Hoto: Washington Informer


MarubuciBello Galadanchi


To idan za ka fara a gida da jarin dubu uku zuwa dubu biyar, me ya kamata ka yi? Kar ka tayar da hankalinka. Hanyoyin suna da sauƙi.


1. KA KOYI GIRKI: Koda ba kai ne za ka ringa girka abincin a shagonka ba, to ya kamata ka san yadda ake girki, yadda za ka fahimci nauyin da ke kan wanda zai ringa girka maka abincin nan gaba. Koyon girki zai ba ka damar fahimtar ƙwarewar sa, buƙatun sa, da kuma tabbatarwa ka ba shi duk abubuwan da yake buƙata domin yin aikinsa yadda ya kamata da samun nasara nan gaba.


2. KA ƘWARANCE A DUKA AYYUKAN DA SUKA SHAFI GIRKI: Wannan zai sa ka fahimci irin ayyukan da ma’aikatanka ko abokan aikin ka za su yi. Za ka fahimci sauƙi ko wahalar aikin. Hakan kuma zai buɗe maka idanu wajen gane yadda za ka ƙarfafawa ma’aikatanka ko abokanka gwiwa. Ka koyi wanke tukwane, da shirya abinci a kan faranti da duk wasu ayyuka da wannan sana’a za ta ƙunsa. Ka tabbatar ka iya duka ayyukan wannan sana’a, yadda za ka iya horas da sababbin ma’aikata, da kuma ganewa idan ɗaya daga cikin su yana yaudararka ko ha’intarka.


3. KA NAZARCI YANAYIN HARKAR ABINCI A UNGUWAR DA KAKE: Akwai sababbin abubuwa dake fitowa kullum, kuma yana da matuƙar muhimmanci ka san ire-iren abubuwan dake ɗaukar hankulan jama’a. Idan akwai wani sabon abu da kake gani za’a samu alheri, to ka yi maza ka koya, kuma ka koya wa ma’aikatanka.


4. KA FAHIMCI LISSAFIN KUƊAƊEN SANA’AR: Jama’a wannan yana da matuƙar muhimmanci. Sana’arka ta abinci ba za ta yi nasara ba kawai saboda abincin yana daɗi, kuma jama’a suna so. A’a, yanke shawarwari masu fa’ida da fahimtar yadda duk fannonin sana’ar ke da nasaba da kuɗaɗen shiga su ne gimshiƙin nasarar ka. 


Saboda haka dole ne ka duba lissafe-lissafen sana’ar, domin sanin abubuwan dake kawo kuɗi, da waɗanda ba sa kawo kuɗi. Duk abin da ba ya kawo kuɗi, to ka yi ƙafar ungulu da shi, ko ka yi kokarin yi masa kwaskwarima yadda zai kawo riba. 


Ka ƙiyasta adadin kuɗaɗen farawa su zama sun fi adadin da kake buƙata, saboda zaman ko-ta-kwana.


5. KA BINCIKI UNGUWAR DA ZA KA FARA WANNAN SANA’A: Ka samu biro da takarda, ka lissafa duk shagunan abinci, da ire-iren abincin da suke sayarwa. Idan ka ga cewa akwai wani nau’in abinci da jama’a suke ci yau da kullum, kuma babu wani shago da ke yinsa, to za ka iya mayar da hankali akai. Kar ka yi ƙoƙarin fara sayar da abincin da kowa yake sayarwa.


6. KA FARA TALLATAWA KAFIN KA FARA SANA’AR: Ka buga fosta, ka aika saƙonnin text, da WhatsApp, da WeChat, ka rataye alama a kofar gidanku kuma ka rubuta ranar da za a fara wannan sana’a. Idan akwai hali, ka gayyaci manyan unguwa da abokai zuwa gidanku ranar da ka fara domin su zo, su saka albarka. Idan ka burge su, to za su gayawa sauran jama’a.


Sirrin duk wani sabon sana’a mai nasara shi ne biyan buƙatun jama’a (wareware musu matsaloli) cikin hanzari, rahusa da mutunci. Allah Ya bada sa’a. Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user