Tuesday 30 July 2024

Hikayar Wani Magidanci Da Surukan Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani mutum ne ya ƙwazzabi matarsa, a kullum sai ya sami hanyar da ya bi ya ci mata mutunci, yana zagin iyayenta anini-anini. Daga ya ce 'duk inda aka fito na tabbata kin haɗa jini da makaɗa', sai ya ce 'wane ɗan gidan ku ya yi mini kama da wani kuturu da na sani.'.


Wani Magidanci Da Surukan Shi
Hoto: Wwambam


MarubuciSadiq Tukur Gwarzo


Haka dai, yana mata matuƙar cin mutunci. Idan dare ya yi ta ce ya raka ta banɗaki sai ya ce 'ai da ma na san ke jikar Yambashirwa ce (wato masu zawayi a kasuwa)'.


Tana nan cikin wannan hali kullum idan ya yi mata sai dai ta haɗe kai da gwiwowi ta yi ta kuka, in ta ƙare ta share hawayenta amma ba ta taɓa gwada rama zaginsa ba. 


Rannan sai ga wani kawunta ya zo ya sanar mata cewa an yi haihuwa a gidansu. Bayan sun gaisa ya sha ruwa, sai ya ce mata, "Amma na ga duk kin rame kamar da ke ake miya".


Yarinya da ta samu kafa sai ta kwashe duk labarin ƙuƙumin da take ciki ta labarta wa kawunta. Da ya ji haka sai ya ce, "Ya yi da gwannai. Ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha. Idan rashin kunya yake taƙama muna marhabin da shi."


Sai ya shawarta mata cewa ta sami lokaci su tafi wurin bikin nan tare da shi.


Ta kuma gaya masa cewa a gidan kawun nata za su sauka.


Hakan ta haddasu.


Ranar biki sai ga yarinya tare da mijinta a gidan kawun nan nata. Aka kawo wa mijin fura da zuma kamar ta harbe shi don zaƙi, ya sha.


Da ƙare sha sai ya ce, "Allah sarkin baiwa, watau ko gidan ƙaho kamar kawun nan naki ana shan fura da zuma. Ko kuwa an yi ne don in za ta ya daina ɗanbashirwanci?"


Ita dai ta kanne, ba ta ce masa komai ba.


Can an jima aka shiga kawo masa nama soyayye mai maiƙo.


Shi kuwa sai ɗorawa yake yana cewa, "Oh, ashe ragon gidan mayu ma yana da mai. Mu dai Allah ya mai da mu gida lafiya kada a yi balangu da kurwar mutum." 


Haka dai aka yi ta kawo masa gara iri-iri shi kuma yana ci yana yankan ƙauna kamar yadda ya saba.


Da dare ya yi lokacin bacci ya zo sai kawun yarinyar ya kira shi ya ce masa,


"Saboda yawan jama'a mun rasa ɗakin da za mu ba ka kai da matarka. Sai dai za mu yi maka shimfiɗa a can ɗakin yara tun da yau ne kawai gobe za ku tafi gida".


Bako ya ce, "Ai ba kome."


Aka je aka yi masa shimfiɗa, sannan aka kira yaran da suke ɗakin aka ce musu in dare ya yi duk abin da suka ji baƙon nan ya yi kada su ce kome.


Bayan kowa ya kwanta sai wani ƙanin yarinyar nan ya tayar da mutumin nan kamar yadda aka shirya masa, ya ce, "Na manta in gaya maka cewa idan dare ya tsala kada ka kuskura ka fita waje ko da sunan tofar da yau/yawu. Dalili kuwa shi ne saboda a ƙauyen nan namu akwai wasu fatalwoyi da suka kai mana ƙul. Duk waɗanda suka gwada fitar dare daga wanda za a tarar an ƙwaƙule wa idanu, sai wanda za a tarar ba hannaye da ƙafafuwa duk an cire, mu dai Allah ya tsare kawai".


Bako ya Ce, "Amin. Ai ka ga gara da na sani yanzu in na kwanta abina sai da asuba ko?"


A bisa wannan shiri sai kawun matar nan ya je ya ɗauko damin karan dawa biyu da ya shirya wata dabara da su. Wannan sai ya ɗaura masa farin zane ɗayan kuwa ya ɗaura masa baƙin zane, ya yi musu wasu 'yan dabaru suka ƙara tsawo.


Idan ka gan su sai ka za ta wasu aljanu ne a tsaye. Ya kawo ya jingine a jikin bango daidai ƙofar ɗakin da baƙon nan yake, ya koma ya kwanta abinsa.


Cikin toye-toyen nan da aka yi wa baƙo da rana ashe an barbaɗa wani maganin sa gudawa an haɗa da ya ji. Can mutumin nan na cikin barci sai magani ya fara aiki. Cikinsa ya murɗa ƙwarrai. 


Mutumi ya tashi zaune yana wani nannauyan numfashi. Can kuma sai ciki ya lafa. Har barci ya soma kama shi sai kuwa cikinsa ya kuma murɗawa.


 Ya zabura.


 A wannan karon fa ciki ya ce bai san rangwame ba.


Tun yana zaune nar ya miƙe tsaye gumi na karyo masa sai runtse ido yake kamar wanda ake caka wa allura.


Da azaba ta yi masa yawa sai ya yi tunanin fita waje ƙila ma fatalwa ba ta zo ba.


Yana buɗe ƙofa sai ya yi kaciɓis da abubuwan nan da kawun yarinya ya kafa. 


Nan da nan ya jawo kyauren ɗaki kub ya mayar ya rufe yana cewa, "Wai!!! yau na yi arziki da an ƙwaƙule idanuna." 


Ciki ya ƙara murɗa wa mutumi tun yana tsaye har ya kai tsugune. 


Da ya ga kamar idan bai yi zawon nan ba zai mutu sai ya ce wa yaran nan, "Kuna ji?",


Ya ga ba su motsa ba. Ya sake cewa,


"Kuna ji?!!"


Ya ga ba su motsa ba. Sai kawai ya kwale ya tsuguna cikin ɗakin nan ya tsulala zawonsa har kashi uku, ya koma ya kwanta abinsa yana cewa "Kai ai gara haka."


Washegari sai babban cikin yaran ya tashi ya ce, "Hm'mm'" ya riƙe hanci, "ga tsinannun yara. Yanzu ku rasa inda za ku baje mana zawayi sai cikin ɗaki? Ku tashi marasa kunya"


Ya doddoke su suka yi waje. 


Da mai gida ya ji ana kaiya kaiya sai ya ce wa babban cikin yaran, "Mene ne ne"?


Sai yaron ya ce, ""Kashi suka yi mana a ɗaki, wajen ba ya shiguwa."


Maigida ya zo ya duba ya ce, ""Kai waɗannan akwai 'yan banza, yanzu ba ku tashi ba ni kunya ba sai da surukai suka zo mana. To duk wanda ya yi zawon nan ya kuka da kansa, don sai na barbaɗa magani cikinsa ya kumbura ya fashe."


Ya tafi yana zage-zage mutanen gida duk suka fito. Ya ɗauko wata jaka ya fitar da wani ƙunshin magani daga cikinta. Ya ce, "Yanzu ina barbaɗa wannan magani cikin ko wane ne ya kumbura tim har ya fashe. Me ake da ɗan da zai kai ka ga kunya?"


Yara wannan ya ce, "Ni dai ba ni ba ne". Wancan ya ce, "Ni dai ban farka ba."


Maigida ya ce, "Ai ko wane ne sai uwashi ta yi kuka." 


Ya damƙo magani zai barbaɗa sai baƙon nan ya riƙe hannunsa ya ce, "Tsaya kawu kada mu yi ɓarna, in dai don ni ne wallahi na yafe. Ka bar su matsuwa ce ta sa su yin haka."


Maigida ya ce, "Ai ba don kai ba, idan na ƙyale gobe ma haka za ta faru. Bari ka gani ko wane kafiri ne yau uwarsa ta rasa shi." Ya yi wuf zai sa magani sai baƙo ya sake riƙe hannunsa ya ce, "Tsaya. Gaskiya 'yar Allah da wannan ɗan ƙaramin na fari ni na yi shi, amma ban san wanda ya yi waɗancan biyun ba,"


Maigida ya ce, "To in kai ka yi shi ai mun san lalura ce. Saboda haka bari a zuba kan wanda ba kai ka yi ba." 


Maigida ya je zai zuba magani a kan kashi, sai baƙo ya riƙe shi, ya ce,


"Dakata, kai wannan ma ina tsammani ni ne na yi shi, amma fa na manta ko ni ne ko ba ni ne ba."


Maigida ya ce, "To tun da ba ka tabbata ba bari a sa kaɗan yadda ko wane ne zai wahala kam amma ba zai mutu ba". 


Mai gida ya yi kamar zai zuba sai bako ya tare shi ya ce, "Tsaya. Don Allah a ɗauka a kan shi ma nine na yi, Amma ka ga wancan, mai yawan can, ba ni na yi shi ba."


Mai gida ya ce, "To, shi ke nan. Tun da ka nuna iya waɗanda ka yi ai ba kome. Shi kuma mai wancan ya mutu sai wani." 


Ya matsa kusa da tarin zawon nan mai yawa ya dumbuzo magani zai sa sai baƙo ya cafke hannunsa ya ce,


"kai tsaya dai in faɗi gaskiya, ko kuwa? Tun da dai nan gidanmu ne ba na wasu ba, ba wani abin ɓoyo. Wannan ma ni na yi shi kada a tsaya ana wahala."


Sai yaran nan duk suka fashe da dariya mai gida ya dubi surukin nan nashi ya ce, "Kai wane irin mutum ne da za ka rasa wurin da za ka yi zawo sai gidan surukanka. Ka gan ka dai ba ka gaji kunya ba. Tun da kuma ka yi mana zawo a nan, ai ba inda ba za ka iya yin zawo ba har a masallaci. To wa ma ya sani ko gado ka yi ba mu sani ba muka ɗauki 'yarmu muka ba ka. Ni ai tun ranar da ka zo nan na dubi idanunka na gan su kamar idanun wanda ya sha nonon maita na ce auren nan a yi dai amma sai ka kai mu ga kunya. Yanzu bari na kira makwabta su gani su shaide mu, ke kuma.."


Ya ce da matar, "ki tafi gidan AIƙali ki yi ƙara.. Kai Sarki ma ya kamata ya ji wannan maganar don a aika har mutanen garinku su zo."


Da mutumin nan ya ji haka sai ya faɗi kwance yana ɗibar ƙasa yana afi yana cewa, "Na tuba na bi Allah na bi ka kawu don Allah ka yi min sutura kada mutanen garinmu su ji." Kawun yarinya ya ce nan fa ɗaya, lallai sai jama'a sun sani. 


Da mijin matar nan ya ga ba Sarki sai Allah sai ya je gabanta ya riƙe ƙafafunta yana cewa ya tuba ita ma ta yi masa gafara kada mutane su sani. 


Can dai da ita da duk sauran matan bikin nan suka shiga ba mai gida haƙuri. Kai da ƙyar dai suka ciwo kansa. Ya ce wa mutumin nan, "To tashi ka tafi garinku kada ka ƙara yin zawo, ka ji ko? Yanzu na yafe ka."


Mutumin nan ya tashi ya dawo gida shi kaɗai. Bayan 'yan kwanaki matarsa ta dawo ta same shi.


Daga ranar nan ko awakin gidan su yarinyar nan ya gani kunyarsu yake ji balle mutane. Ita kuma daga lokacin nan ta sami lafiya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user