Thursday 25 July 2024

Hikayar Wani Sarki Da Babban Aminin Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

An hakaito cewa, sa'adda Sarki Ahmad, ɗaya daga cikin sarakunan Daular Usmaniyya, ya yi shirin zuwa yaƙi. Sai ya kira babban amininsa, kuma na hannun damansa, Musa. Ya damƙa masa wani ɗan mabuɗi ya ce masa, "Ungo wannan ka ajiye shi wajenka. Idan aka kwana huɗu ban dawo ba, to ni tawa ta ƙare. Ka tafi gidana na lambu ka buɗe shi. Akwai zaɓaɓɓun kuyangina a ciki, ka kwashe su duka na ba ka."


Sarki Da Babban Aminin Shi
Hoto: Wikipedia


MarubuciBukar Mada


Suka yi sallama. Sarki ya hau doki, ya bi rundunar yaƙi. Can bayan kamar sa'a guda suna tafiya, sai Sarki ya hango ƙura daga bayansu, ta tokare sararin samaniya. Zuwa can sai ya ga ashe wani mahayi ne ke cin ingarma.


Da mai dokin ya iso inda Sarki, sai ya ga ashe abokinsa ne Musa. Sarki ya tambaye shi, lafiya ya biyo su?


Musa ya kada baki ya ce, "Allah ya ba ka nasara, mabuɗin da ka ba ni ba shi ne mabuɗin lambun ba."


Sarki ya yi tsaye cike da mamaki yana tunani. Ashe haka duniya take? Tun ban mutu ba ke nan ake nema a mallaki dukiyata? Babban abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne, abokinsa da ya amince wa fiye da kowa, shi ne ya kasa haƙurin kwana ɗaya, ballantana haƙurin kwana huɗu, kafin ya fito da maitarsa a fili.


Don haka 'yan uwa sai ku kula sosai da irin mutanen da kuke bai wa amana.


Sau da yawa makashinka na nan tare da kai.


An kuma ce, munafukinka, tabarmarka!

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user