Na kyautar da soyayyata ga wadda ta cancanta da wannan babbar kyauta.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Ita ce wadda idanuwa ba sa gajiya da ganin kyakkyawar fuskar ta.
Ita ce wadda kunnuwa ba sa ƙosawa da jin
zazzaƙar muryar ta.
Ita ce wadda tafiyar ta ke zama abar yabo da kallo a lokacin sassanyar iskar yammaci.
Ita ce wadda sautin muryar ta idan ya ratsa
dodon kunne sai a ji kamar busar zazzaƙar
sarewar aljanu ce.
Ita ce ma'abociyar yalwar gashin gira baƙi siɗik da ƙyallin haƙori da lotsawar kunci idan ta yi murmushi.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.