Thursday 11 July 2024

Karanta Addu'ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana'iza

Tura Wannan Zuwa Ga


اَللَّهُمِّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدْ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا نَقّيْتَ الثَّوْبُ اْلأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَس، وَأَبْدِلْهُ دَاراً خَيْراً مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلاً خَيْراً مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجًا خَيْراً مِنْ زَوْجِهِ، وَأَدْخِلْهُ الْجَنَّةَ، وَأَعِذْهُ مِنْ عَذابِ القَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ.


Addu'ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana'iza
Hoto: Nigerian tracker


Allahummagh-fir lahu warhamh, wa'afihi, wa'fu 'anh, wa-akrim nuzulah, wawassi' mudkhalah, waghsilhu bilma-i waththalji walbarad, wanakkihi minal-khataya kama naqqaytath-thawbal-abyada minad-danas, wa-abdilhu daran khayran min darih, wa-ahlan khayran min ahlih wazawjan khayran min zawjih, wa-adkhilhul-jannah, wa-a'izhu min 'azabil-kabr, wa'azabin-nar.


Ya Allah! Ka yi masa gafara, Ka ji kansa, Ka amintar das hi daga bala'i, ka yi masa rangwame, kuma Ka girmama lafiyarsa, ka yalwata mashigarsa (kabarinsa), kuma Ka wanke shi da ruwa da kankara da ruwan raba, Ka tsaftace shi daga laifuffuka kamar lyadda Kake tsaftace farar tufa daga dauda, kuma Ka musanya masa gidan da yafi gidansa alheri, da mutanen gida da suka fi mutanen gidansa alheri, da mata da ta fi matarsa alheri, kuma Ka shigar da shi Aljanna, ka tsirar da shi daga azabar kabari da azabar wuta.


اَللَّهُمِّ اغْفِرْ لِحَيِّنَا وَمَيِّتِنَا وَشَاهِدِنَا، وَغَائِبِنَا، وَصَغِيرِنَا وَكَبِيرِنَا، وَذَكَرِنَا وَأُنْثَانَا. اَللَّهُمِّ مَنْ أَحْيَيْتَهُ مِنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى اْلإِسْلاَمِ، وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَّا فَتَوَفَّهُ عَلَى اْلإِيمَانِ، اَللَّهُمِّ لاَ تَحْرِمْنَا أَجْرَهُ، وَلاَ تُضِلَّنَا بَعْدَهُ.


Allahummagh-fir lihayyina wamayyitina washahidina, wagha-ibina, wasagheerina wakabeerina, wathakarina wa-onthana. Allahumma man ahyaytahu minna fa-ahyihi 'alal-islam, waman tawaffaytahu minna fatawaffahu 'alal-eeman, allahumma la tahrimna ajrah, wala tudillana ba'dah.


Ya Allah! Ka gafarta wa rayayyunmu da matattaunmu, da wadanda suke halarce tare da mu da wadanda ba sa nan da yaranmu da manyanmu, da mazajenmu da matayenmu, ya Allah! Wanda ka rayar das hi daga cikinmu, to Ka rayar da shi a cikin Musulunci, wanda kuma ka dauki ransa, to Ka dauki ransa a kan imani. Ya Allah! Kada ka haramta mana ladan (hakurin rashinsa), kada kuma ka batar damu bayansa.


اَللَّهُمّ إِنَّ فُلاَنَ بْنَ فُلانٍ فِي ذِمَّتِكَ، وَحَبْلِ جِوَارِكَ، فَقِهِ مِنْ فِتْنَةِ الْقَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ، وَأَنْتَ أَهْلُ الْوَفَاءِ وَالْحَقِّ، فَاغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ.


Allahumma inna (fulanin) fee zimmatik, wahabli jiwarik, faqihi min fitnatil-kabr wa'azabin-nar, wa-anta ahlul-wafa', walhak, faghfir lahu warhamh, innaka antal-ghafoorur-raheem.


Ya Allah! Hakika wane dan wane yana cikin alkawarinka (na kiyayewa) da amanarka; don haka Ka tserar da shi daga fitinar kabari da azabar wuta. Kai ne ma'abocin cika alkawari da gaskiya; Ka gafarta masa, Ka ji kansa. Hakika Kai, Kai ne Mai yawan gafara, mai yawan jin kai.


اَللَّهُمِّ عَبْدُكَ وَابْنُ أَمَتِكَ، اِحْتَاجَ إِلَى رَحْمَتِكَ، وَأَنْتَ غَنِيٌّ عَنْ عَذَابِهِ، إِنْ كَانَ مُحْسِناً فَزِدْ فِي حَسَنَاتِهِ، وَإِنْ كَانَ مُسِيئاً فَتَجَاوَزْ عَنْهُ.


Allahumma 'abduka wabnu amatik, ihtaja ila rahmatik, wa-anta ghaniyyun 'an 'azabih, in kana muhsinan fazid fee hasanatih, wa-in kana museean fatajawaz 'anh.


Ya Allah! Bawanka kuma dan baiwarka ya bukatu ga rahamarka, kuma mawadaci ne ga barin azabarsa, idan mai kyautata aiki ne, Ka yi kari a cikin kyawawan ayyukansa, idan kuma mai mummunan aiki ne, Ka yafe masa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user