Riya ( yin abu ba don Allah ba) a wurin neman ilimi yana da alamomin da ake ganewa ya kamata ɗalibai su nisance shi.
Marubuci: Ibrahim Nuhu Imam Rimi
1- Idan ya zama kana son yabo da jinjina akan abun da ka yi wurin neman ilimin.
2- Idan ya zama kana son ɗaukaka a cikin mutane saboda a ce kai ɗalibin ilimi ne.
3- Idan ya zama kana yi wa mutane girman kai, kuma kana ganin ka fi kowa.
4- Idan ya zama ba ka amsar nasiha da karɓar gyara.
ﺍﻟﺮﻳﺎﺀ ﻓﻲ ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻟﻪ ﻋﻼﻣﺎﺕ ﻓﺎﺣﺬﺭﻫﺎ؛ ﻓﻤﻨﻬﺎ.
1 : ﺃﻥ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻤﺪﺡ ﻭﺍﻟﺜﻨﺎﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺍﻟﺘﻲ ﺗﻤﺎﺭﺳﻬﺎ ﻓﻲ ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ.
2 . ﻣﺤﺒﺔ ﺍﻟﻈﻬﻮﺭ ﺃﻣﺎﻡ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻷﻧﻚ ﺗﺘﻤﻴﺰ ﺑﻄﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ.
3 . ﺍﻟﺘﻜﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻭﺃﻥ ﺗﺮﻯ ﻧﻔﺴﻚ ﺑﻌﻴﻦ ﺍﻟﻜﻤﺎﻝ.
4 . ﻛﺮﺍﻫﻴﺔ ﺍﻟﻨﺼﻴﺤﺔ ﻭﺍﻟﺘﻮﺟﻴﻪ.
Ku koyi ilimi kuma ku koyar da mutane, ku koyi kamun kai da natsuwa, ku koyi sauƙin kai ga wanda kuke koyo a wurinsa da wanda kuke koya ma, kar ku zamo malamai masu jiji-da-kai , sai jahilcinku ya bayyana a kan iliminku - Umar bn khaddab
ﺗﻌﻠﻤﻮﺍ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭ ﻋﻠﻤﻮﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ,
ﻭ ﺗﻌﻠﻤﻮﺍ ﺍﻟﻮﻗﺎﺭ ﻭ ﺍﻟﺴﻜﻴﻨﺔ ,
ﻭﺗﻮﺍﺿﻌﻮﺍ ﻟﻤﻦ ﺗﻌﻠﻤﺘﻢ ﻣﻨﻪ ﻭ ﻟﻤﻦ ﻋﻠﻤﺘﻤﻮﻩ ,
ﻭﻻ ﺗﻜﻮﻧﻮﺍ ﺟﺒﺎﺭﺓ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﻓﻼ ﻳﻘﻮﻡ ﺟﻬﻠﻜﻢ ﺑﻌﻠﻤﻜﻢ
ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ