Sunday, 21 July 2024

Karanta Dadadan Kalaman Soyayya Masu Kwantar Da Hankalin Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

A cikin ƙasaitaccen lambu mai cike da ni'ima, a lokacin da yammaci ke saukar da daddaɗar iska, bishiyu na rangaji, ganyayyakinsu na bugar juna, tsuntsaye suna tashi daga kan wannan ice/itace su koma kan wancan, suna sakin daddaɗan kukansu, kyawawan furanni masu jan hankali gami da ƙamshi ke zubowa daga kan bishiyoyin, ƙamshin su yana ƙamsasa duniya, kyakkyawan ruwan ƙorama mai haske na kwarara suna bin tsakanin duwatsu. 


Daɗaɗan Kalaman Soyayya Masu Kwantar Da Hankalin Masoya
Hoto: Connie Rizzo 


MarubuciImran Musa Jahun


A daidai wannan lokacin soyayyarki tana ƙara narkuwa a cikin ɓargo da jinina, duk bayan gushewar kowace daƙika (second). 


Tunaninki a duk giftawar ƙwayar zarra ƙara yawaita yake, yana azabtar da ƙwaƙwalwata fiye da komai. 


Ambaton ki a kowanne lokaci, a  koyaushe shi ne a kan harshena da yake gudana a cikin bakina. 


Idanuwana a koyaushe babu abin da suke buri da muradi illa kwaɗaituwa da son kallon kyakkyawar fuskar masoyiyata. 


Hoton ki shi ne zai zamanto abokin hirata a duk lokacin kwanciya baccina. 


Masoyiyata ta gobe soyayyarki tana jone da rai, rabuwarsu kuwa sai ranar fitar numfashina. 


Kada ki ƙi ni duk rintsi da tsanani. 


Don ALLAH masoyiyata ta gobe ki

girmama ƙaunata a cikin zuciyarki, ki tarairayi begena a cikin ruhinki, sunana ya zamo dawwamamme a bakin ki. 


Sannan ina roƙon ki cewa idanuwan ki 

su ƙauracewa kallon dukkan wani ɗa namiji a duniya idan ba ni ba. 


Na fi son ki da ƙaunarki fiye da komai a rayuwata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user