Bari mu fara da bambance “bada” bashi da “karɓar” bashi a wannan rubutu. Bayar da bashi na nufin ɗaukar kayan da ake sana’a da su, a bai wa wani ba tare da ya biya kuɗin kayan baƙi ɗaya ba. Karbar bashi yana nufin samun aron kuɗi daga banki ko wani da nufin taimakawa mai fara sana’a.
Marubuci: Bello Galadanchi
Yanzu zamu mayar da hankali ne a kan illar BADA bashi ga sana’a.
Bari na ba ku labarin Buji da Hutti.
Buji bafillatanin saurayi ne mai buri. Ɗan shekaru 13, ya ɗauki aniyar koyon sana’a, domin ya kasance yana da abun yi, ya dogara da kansa, sannan ya samu kuɗaɗen kashewa. Burinsa shi ne ya mallaki shanu dubu biyu. Da yake iyayensa ba su da ƙarfi sosai, shi ne ya tattara ‘yan kuɗaɗensa baki ɗaya ya sayo saniya. Kowace safiya, sai ya tatsi nonon wannan saniya, ya sayar wa ‘yan unguwa, sannan ya yi amfani da kuɗin ya sayowa saniyar harawa. ‘Yan kuɗaɗen da suka rage, sai ya raba biyu, kashi ɗaya ya yi amfani da shi, ɗaya kashin kuwa ya adana. Haka ya ci-gaba da maimaitawa har tsawon shekara ɗaya, sannan kuɗinsa ya taru, ya sayo bujimin sa, ya haɗa da saniyarsa. Ba’a yi shekaru uku ba, Buji yana da shanu goma.
A hankali bayan shekaru 10, Buji ya tara shanu ɗari bakwai da hamsin da shida. Shanunsa na haihuwa, adadin nono na ƙaruwa, har kamfanonin madara ne suke sarar nono a wajensa su biya shi nan take. Shi kuma sai ya ƙaro dabbobi, da awaki, da kaji. Yanzu haka yana da yara sama da hamsin masu taimaka masa, da matan aure goma sha biyar, da ma’aikata manya maza su ashirin da biyu. Saboda arzikin da yake samu, kowace shekara yana zakka, yana sadaka, sannan yana kai ‘yan garin su aikin hajji.
A ɗaya ɓangaren kuwa, Hutti shi ma ya sayo saniya a lokaci ɗaya da Buji. Kamar Buji, Hutti yaro ne mai buri da kirki sosai. Ya sayo saniyar a lokaci ɗaya da Buji, mutanen garin su kuwa sai murna. Da ya fara tatsar nono yana talla, sai ‘yan uwanshi da abokai waɗanda ya yi wa talla su ce ba su da kuɗi, amma idan har ya ba su nono, to za su biya shi a mako mai zuwa. Tun yana cewa a’a, har ya fara yarda. To da yake ba ya samun kuɗaɗen sayar da nono nan take, sai ya kasance babu isassun kuɗaɗen sayo harawa a domin bai wa saniya. Adadin nono kuwa ya fara raguwa, saniya ba ta samun isashen abinci. Shi kuwa Hutti, duk kirkinsa, sai ya fara bin mutanen da ya bai wa bashi yana tambayarsu, su kuwa suna gaya masa ya dawo gobe ko jibi.
Rashin lafiya ya kama saniya, saboda haka dole ya sayar da rediyon shi domin sayo wa saniya magani da harawa. Idan kuwa jama’a suka tashi, sai su ba shi kuɗi ɗan kaɗan, su ce masa ya dawo gobe. ‘Yan kuɗaɗen da yake karɓa a wajensu ba su taka kara sun karya ba, shi kuma sai ya ringa kashe su domin sayen abincin da zai ci.
Daga baya idan mutanen da yake bi bashi suka ganshi, sai su ringa ɓoyewa, ko suna kau da kai, ko kuma raina masa hankali. Duk sai annurin fuskar Hutti ya koma duhu, ya rasa abin da yake masa daɗi a duniya. Rashin lafiyar saniyar shi ya fara tsanani har ya fara tunanin sayar da ita, ko kuma ya yanka ta ya sayar da naman. A haka, zai rage asara. Ba’a yi mako ɗaya ba, wata asuba yana shiga kangon saniyar, sai gawar ya tarar.
A wannan labari, saniya ita ce sana’a. Nono shi ne kuɗaɗen shigar wannan sana’a. Dole sai an sayar da nono kuma an tara kuɗi kafin sabuwar sana’a ta bunƙasa. Buji ya fahimci haka, amma Hutti bai fahimta ba. Kar ka zama Hutti, ka zama Buji. Idan har ka bada nonon saniyar ka bashi, to saniyar ba za ta ba ka isasshen nono ba. Idan kuwa babu nono, to ba za ka iya ciyar da saniyar ba, balle ta ba ka nono. Idan kuwa ba ta bada nono, to ta zama wahala a gare ka, saboda dole ka ciyar da ita.
GARGAƊI
Ka fahimci dalilin da yasa kake sana’a. Babu alaƙa tsakanin sana’arka da ‘yan uwantaka ko abokantaka. Idan wani ɗan uwa ko aboki yana neman taimako, ka rage masa kuɗi, amma sai dai ya biya nan take. Idan ba shi da kuɗi, kar ka ba shi nono.
Idan ka ba shi nono, to saniya ba za ta samu isasshen abinci ba. Mutanen da suke biyan kuɗi nan take su ne kwastomominka. Kar ka yaudari kanka. Idan mutum bai ba ka kuɗi nan take ba, to ba kwastoma ba ne.
Idan ka rabawa mutane talatin kayanka, amma mutum huɗu ne kawai suka biya ka nan take, to mutum huɗu ne kawai kwastomominka masu so ka ci-gaba.
Gishirin ci gaban sana’a shi ne juya kuɗaɗen da sauri yadda za su ringa ƙaruwa. Bashi kuwa ƙaton rami ne akan titin kasuwanci. Ko kana so, ko ba ka so, zai rage maka gudu, ko ma ya dakatar da kai baki ɗaya. Idan ba ka yi sa’a ba, ka zurma cikin ramin.
Kar ka ba wa kowa bashi, ko ciki ɗaya kuka fito. Idan mutum ba shi da kuɗin biya, to ya yi haƙuri har sai Allah Ya hore masa. Idan sadaka za ka yi, to wannan kuma wani abu ne daban, amma kar ka cutar da saniyarka har ka zama silar mutuwarta. Ka tabbatar kana da issashen nonon da zai ciyar da ita ba tare da yunwa ya kamata ba.