Monday, 29 July 2024

Karanta Zafafan Gajerun Kalaman Soyayya Na Barka Da Dare

Tura Wannan Zuwa Ga

Saƙonnin mu kwana lafiya tsakanin masoya, saƙonni ne da suke da tasiri a tsakaninsu.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Barka Da Dare
Hoto: Wallpapers

Marubuci:- Abdul A U Tonga


Duk masoyan da suka saba yi wa junansu irin waɗannan saƙonnin, zai yi matuƙar wuya bacci ya ɗaukesu ba tare da sun karanta irin wannan saƙon daga masoyansu ba.


Ga wasu saƙonnin nan da masoya za su iya turawa junansu domin inganta soyayyar su.


1. Na kan yi takaici idan dare ya yi, saboda sai na yi wasu awanni/sa'o'i ba tare da jin ki ko ganin ki ba. Da fatan za ki tashi lafiya.


2. Ina miki fatan yin mafarki mai daɗi da kuma kyau tamkar fuskarki.


3. Babu yadda za a iya kwantanta ganin ki a mafarki da kuma ganin ki a zahiri. Da fatan da ke zan soma arba idan Allah ya tashe mu lafiya.


4. A kullum, a daidai irin wannan lokacin na kan yi burin ganin lokacin auren mu ya gabato.


5. Duk abubuwan dake cikin ɗakina, gidana, duk a banza nake ganin su har sai ranar da zan gan ki a tsakar dare a tare da ni a matsayin miji da mata.


6. Gani nake kamar agogo ba ya juyawa saboda yadda na ƙosa gari ya waye idanuwana su gan ki.


7. Zuciyata ta saba da karanta saƙonki, kafin ƙwaƙwalwata ta amincewa idanuwa su rintsa. 


Ina jiran ji daga gare ki kafin na iya bacci.


8. Idan ina son dare ya mini gajarta na soma tunaninki cikin dare.


9. Muddin ba ke ce abu na ƙarshe da na tunano ba, ba ni ba bacci a wannan daren.


10. Sai dare ya yi a irin wannan lokacin nake ƙara tabbatar da dalilin da ya sa nake son ki.


Namiji zai iya aikawa mace, ita ma mace za ta iya aikawa namiji ba wai na maza ba ne kaɗai.


Da fatan za a yi soyayya mai tsafta domin samun zaman aure da zuri'a masu tsafta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user