Thursday, 11 July 2024

Kyakkyawar Nasiha Ga Sabon Ango

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya ɗan uwana, ina yi maka nasiha da ka ji tsoron Allah (S.W.T) dangane da wannan amana da ka nema, kuma aka ga cancantar ka karɓe ta; aka ba ka. Ina mai taya ka da addu'a Allah ya ba ikon riƙe wannan amana.


NASIHA A GARE KA ƊAN UWA ANGO
Hoto: Domty


Marubuci:- Aminu Bala


Ka sani cewa aure al'amari ne babba da yake kawo alkhairi duniya da lahira. 


Samun alherin duniya yana tattare da samun nutsuwa ta cikin gidan; samun alherin lahira kuma yana tare da bin dokokin Ubangiji sau da ƙafa. Don haka, ba za ka samu nutsuwa a cikin gidanka ba, har sai ka yi tanadin hakan. Ka kasance ka tsarkake niyyarka da fatan za ka zauna da ita wannan yarinya da aka aura maka har ya zuwa ƙarshen rayuwarka, ko ta ta rayuwar.


Ka sani cewa ka rabo wannan matar daga gidansu, inda ta fi sabo da shi. Amma saboda son dacewar ta da Allah (S.W.T) ta zaɓi ta ajiye wancan sabo, ta zauna da kai. Da wannan tunani ne za ka dinga bada uzuri a lokacin da ta yi ganganci, ko wauta.


Ina mai yi maka nasiha da cewa ka sani cewa kodayake wannan matar ta zaɓi ta baro gidansu ta zauna tare da kai, amma dai zuciyarta ba ta bar su ba, saboda haka ka taimaka mata a wajen dukkan abin da ya shafi iyayenta da danginta.


Ka sani cewa, yanzu dole ne ka ɗauki matsayi na gurbin waɗanda ta baro su domin ka. A nan za ka dinga cancanzawa lokaci-lokaci. A wani lokacin ana buƙatar ka ɗauki matsayi na mahaifi, ta hanyar yi mata nasiha, a wani lokaci ma a yi mata faɗa domin gyarata. A wani lokaci kuma, za ka zama kamar yayanta ko ƙaninta. Wato ana buƙatar ka ɗauke mata kewar nan da ta rasa na cewa a da tana da waɗannan 'yan uwan nata suna rayuwa da jin daɗi irin na duniya da kuma abin da ya shafi rayuwarsu ta cikin gida.


A wani lokaci kuma, ka zauna da ita tamkar ƙawarta, wadda su kan zauna su yi hira, su yi nishaɗi da barkwanci. A wani lokaci kuma, sai ka zama maigida, tsayayye wanda ba ta da wani wanda zai iya ba ta nutsuwa da kwanciyar hankali kamar ka.


Haƙiƙa bincike ya nuna cewa rashin samuwar waɗannan a cikin gidaje shi yake kawo matsaloli da ba'a iya shawo kansu.


Ina mai tunatar da kai cewa duk yayinda aka rasa wani abu kyakkyawa, to mummuna zai maye gurbinsa. Don haka, wasu daga cikin mazaje suna sakaci wajen nunawa matayensu soyayya sai wannan ya sa su samu kishiyoyi game da soyayyar matan nasu, wato su samu wasu da ke tausayawa da saurarensu tare da nuna musu ƙauna, sai su mance da mazajen nasu, sai miji ya yi ta kishi da waɗancan mutane. Wani namijin ma, da mahaifiyar matar ta sa yake kishi. 


Ya ɗan uwana, a ƙarshe ina mai maka nasiha da ka yi kishin matar da ka aura. 


Kada ka mayar da gidanka kasuwa, wato inda kowa ke da iko ya shiga babu izini. 


Annabi (S.A.W) da aka tambaye shi a kan ƙanin miji ya dinga shiga gurin matar wansa, sai ya kamanta hakan da mutuwa, ballantana abokanai maza da ba su da mahalli a cikin gidanka.


Haka kuma Annabi (S.A.W) ya bayyana cewa mutumin da ba shi da kishin matarsa ba zai shaƙi ƙamshin Aljannah ba. Allah ya tsare mu.


ALLAH YA ALBARKACI AURENKA, YA BA KU ZURIYA KYAKKYAWA; KUMA YA HORE MAKA YADDA ZA KA RIƘE IYALANKA AMIN.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user