A wata kotu ne ana sauraron ƙara jama'a cike maƙil, sai aka buƙaci wata tsohuwa ta fito domin bayar da shaida ga wanda ya kawo ƙara.
Da ta fito sai Lauyan wanda ake ƙara
ya fito domin yi mata tambayoyi.
Lauya: Baaba shin ko kin san ni Wane ne?
Tsohuwa: eh mana na san ka, ai tun kana ƙarami kai maƙaryaci ne, ka iya haɗa waje, ga ka da yaudara da kuma rashin iya magana ga kuma shaye-shaye da neman mata.
Lauya jikin shi ya yi sanyi cikin jin kunya
ya je kusa da ɗayan Lauyan sai ya ce "Baaba wannan fa? kin san shi?
Tsohuwa: ai gwanda kaima. Wannan kam ai asalin daƙiƙi ne gashi da son jin gulma ga kuma munafurci. Kai bari ka ji yanzu haka yana cin amanar matarsa da wasu matan banza har uku kuma ɗaya daga cikinsu matarka ce.
Tana rufe baki sai Alƙali ya kira duka Lauyoyin cikin ƙanƙanuwar murya ta sirri ya ce dasu: "Kun san Allah! idan wani shege daga cikin ku ya kuskura ya tambayeta ko ta san ni, tabbass zai ci ubanshi kuma sai na sa an ƙwace lasisin shi".
Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba.