Bayan dogon lokaci da Alƙalin ya kwashe yana rubutu a cikin ɗimemen littafin da ke gabansa, sai ya ɗago da kansa ya dubi dattijon da ke tsaye cikin akwatin tuhuma, ya ce masa, "Malam Kalla ka ji abin da Malam Tanimu yake tuhumarka da shi. Ka ce wai shi maye ne, wanda hakan ya jawo masa ɓacin suna da baƙin jini a cikin jama'a.
Marubuci: Bukar Mada
Dattijon da ake tuhuma ya kalli alƙali, fuskarsa duk ta nashe da gumi kamar wanda ya haɗiye kunama da ranta. Da ma an ce mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi. Ya ce, "Iye, na'am! Allah gafarta Malam, Wallahi ni da wasa na ce masa maye, suɓul da baka ne kurum na yi. Kuma wannan 'yar magana da na faɗa a majalisa, tun da ba rariya na bi ina shela ba, ta yaya za ta yaɗu har ta ɓata masa suna? Da ma dai akwai azazza tsakaninmu, Allah ya taimake ka."
Alƙali ya ci gaba da rubutu a cikin littafin da ke gabansa. Bayan ya kammala rubuta abin da yake son rubutawa, ko kuskure ya yi a wajen rubutun nasa, sai ya yage takardar ya kekketa ta guntu-guntu. Ya ce wa mai ƙara da wanda ake ƙara su tafi sai gobe su dawo, zai yanke hukunci. Da za su fita sai ya kwashi guntayen takardun nan ya ba Malam Kalla ya ce masa ya watsar da su waje.
Washegari da suka dawo, sai Alƙali ya ce wa Malam Kalla, "Kafin na yanke hukunci, ina so ka fita yanzu ka tattaro mini guntayen takardun nan da na ba ka jiya na ce ka watsar. Kada ka baro guntu ko ɗaya, ka dawo mini da su duka."
Malam Kalla ya tafi, jim kaɗan sai ga shi ya dawo. Ya dubi Alƙali ya ce, "Allah gafarta Malam, ban ga takarda ko ɗaya ba, ina tsammanin iska ta kora su wani waje."
Alƙali ya ce masa, "to ka ga kamar yadda ka watsar da takardun nan wuri guda, amma iska ta kwashe su ta watsa su zuwa lungu da saƙo na garin nan, kuma ka kasa tattaro su. Haka maganar da ka faɗa a majalisa za ta yaɗu zuwa kowane saƙo da lungu na garin nan, kuma ba za ka iya bin kowa ka faɗa masa cewa abin da ka faɗa ƙarya ce ba. Don haka idan ana hira a majalisa, ko dai ka faɗi alheri ko ka ja bakinka ka yi shiru. Magana zarar bunu ce, idan ta fito ba ta komawa."
Alƙali ya buɗe littafi ya fara sabon rubutu, kafin ya yanke hukunci.