Monday, 29 July 2024

Labarin Wani Dalibi Da Malamin Jami'a

Tura Wannan Zuwa Ga

Shekaru goma sha biyu da suka wuce, lokacin da sakamakon ƙarshe na kammala digirinmu zai fito, duka 'yan ajinmu sun saki karin cewa ni ne ɗalibi na farko a tarihin Tsangayar Nazarin Kimiyyar Kwamfuta da zai fita da sakamako mai daraja ta ɗaya. To, amma sai ga ni da sakamako mai daraja ta biyu.


Wani Dalibi Da Malamin Jami'a
Hoto: Study Pug


MarubuciBukar Mada


Ban yi mamaki ba, saboda na sani sarai Dakta Irukefe na nan tamke da bakansa, muddin iska na zagaya huhunsa ba zai taɓa bari na zama wani abu ba. Kamar yadda ya taɓa ce mini, "sai na ga tsiyar da za ka zama a cikin ilmin kwamfuta!" 


Ba kuwa komai ya sa yake gani na da baƙin fenti ba sai don wani ɗan gyara da na taɓa yi masa yayin da yake yi mana lacca cikin aji. Ashe bai ji daɗin gyaran ba, wai na tozarta shi. Hatta bautar ƙasa da zan yi, sai da ya yi kutunguilar da aka tura ni jihar da ba ita na so zuwa ba. 


A cikin satinmu na ƙarshe a sansanin horar da 'yan bautar ƙasa wani mutum ya zo da kwamfuta yana neman wanda zai gyara masa. Na karɓa na gyara masa nan take. Ya yi godiya, ya karɓi lambar wayata ya tafi.


Ashe mutumin nan yaron Sanata ne, maigidansa ne ya aiko shi da kwamfutar. Saboda jin daɗin gyaran da na yi masa sai ya sa aka tura ni ofishinsa don yin bautar ƙasa. Nan take ya ɗauke ni aiki a matsayin mataimakinsa na musamman, ya yanka mini albashi. Aka ba ni gida da motar da zan riƙa zaga gari.


Bayan mun kammala bautar ƙasa, sai Sanatan nan ya riƙe ni. Ya samar mini tallafin ƙaro karatu a Turai na yi digiri na biyu na kuma yi digirin digirgir a kan sha'anin kwamfuta. Cikin shekaru goma sha biyun nan sunana ya yi tambari a ciki da wajen ƙasar nan, ko'ina sai kirana ake yi ina ba da lacca. 


Wata rana na gama ba da lacca a wani gangamin masana kwamfuta na duniya a ƙasar Japan. Na sauko daga kan mumbari sai na hangi tsohon malamina, Dakta Irukefe, a cikin mahalarta taron. Na nufi wurinsa na gaisar da shi, amma ya nuna sam bai gane ni ba. Na tuna masa da kalaman da ya taɓa yi min na ce, "ni ne ɗalibin da ka taɓa cewa, 'sai na ga tsiyar da za ka zama a cikin ilmin kwamfuta.'" Ya cika da mamaki. 


Na ci gaba da cewa, "ina ba ka shawara Malam, ka zama mai ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa, kada ka zama mai cutar da su, domin ba ka san abin da za su zama ba a gaba. Ka ga dai yadda Allah ya ɗaukaka ni, duniya gaba ɗaya an san da ni ta ɓangaren kwamfuta.


Sannan abin da ba ka sani ba, ni na biya kuɗin da aka ɗauki nauyin zuwanka wannan taro. Kuma zan ci gaba da biya maka duk shekara, domin nuna maka godiyata a kan ƙoƙarinka na tura ni bautar ƙasa jihar da ta zama silar wannan ci gaban nawa, kodayake ba da niyyar alheri ka yi ba, amma Allah ya mayar da shi alheri gare ni." 


Ban jira ya ce wani abu ba, na yi gaba abina, na bar shi nan tsaye yana nazarin maganata. Daga baya ya turo mini da saƙo yana ba ni haƙuri.


Don haka, ɗan uwana, kada ka kula da sharrin mai sharri, kai dai yi aiki tuƙuru domin ganin ka cim ma burinka, arzikin duk da Allah ya ƙaddara wa bawa, babu mai iya tare shi. Sara da sassaƙa ba su hana wa gamji toho.


Godiya ga DR. Auwal Aminu Gezawa da ya aiko mini da wannan labari da Turanci. Na taƙaita na kuma fassara shi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user