Abu ɗaya za ka fahimta game da abokan mu'amalarka, sai ka hutar da ranka, ka kuma sha maganin zama da su.
Marubuci:- Abuna'Ila Saminu
Abin kuwa shi ne; ka gane cewa sun kasu gida uku:-
1. Masoyi.
2. Maƙiyi.
3. Mahassadi.
FASHIN BAƘI:-
MASOYI
Shi wannan babu abin da yake yi maka fata illa ci-gaban rayuwarka, farin cikinka da kuma murna da duk abin alkhairin da ya shafe ka, yana taya ka murna, ya kuma taya ka baƙin ciki.
MAƘIYI
Shi kuwa ba ya ƙaunar ka, ba abin da ya dame shi da kai, ko zancenka ba ya son ji, ba ya taya ka murna ko baƙin ciki, ya kan yi murna idan ya ji wani abin baƙin ciki ya same ka, ba ya son jin labarin abin farin cikin da ya same ka, yana kuma nuna maka gaba ƙarara, ba ya munafuntar ka ko kaɗan, domin ba ya gudun ka san ƙiyayyar da ya ke yi maka, ba kuma ya son kusantar duk wurin da ka ke.
MAHASSADI
Shi wannan ganin ƙyashi yake yi maka, ba ya taɓa son ci-gabanka, ba ya farin ciki da duk wata baiwa ko ni'imar da Allah ya yi maka, fatansa ya ga wannan baiwar ko ni'imar da aka yi maka ta gushe, koda kuwa ba za ta koma wurinsa ba, ba ya so ya ji ana yabon ka, ransa kan ɓaci idan ya ga ƙaruwarka, kullum yana cikin bibiyar lamarinka, yana kuma hanƙoron ya ga ya kusance ka, domin hakan ne zai ba shi damar sanin duk wani abu da ya shafe ka, amma kuma ba ya fitowa zahiri ya nuna maka a gabanka, ba kuma ya son ka gano matsayinsa game da kai, ko abubuwan da yake yi maka.
DUBA WANNAN: RAYUWA DA ABOKAI (2)
A kashi na gaba, Insha Allahu, za mu yi bayanin dalilan da suke jawo samuwar kowanne ɗaya daga cikin abokan mu'amalar nan naka, da ma yadda ya kamata ka yi wa kowanne ɗayansu mu'amala. Idan matsayinsa ya bayyana gare ka.