Friday, 12 July 2024

Rayuwa Da Abokai (2)

Tura Wannan Zuwa Ga

A kashin da ya gabata mun yi bayanin cewa, abokan mu'amalarka sun kasu uku: masoya, maƙiya da mahassada.


Mu'amala da abokai
Hoto: Telegraph


Marubuci:- Abuna'Ila Saminu


Mun kuma yi bayanin yadda kowanne kaso yake takunsa dangane da yin mu'amalarsa da kai.


A wannan kashin insha Allahu za mu yi bayanin dalilan da suke jawo samuwar kowanne ɗaya daga cikin abokan mu'amalar naka da muka zayyana, da ma yadda ya kamata ka yi wa kowanne ɗayansu mu'amala, idan matsayinsa ya bayyana gare ka.


DALILAI

Kowanne daga kason abokan nan naka akwai dalilin da ya sa ya zama yadda yake game da kai, kamar haka:-

MASOYI

Dalilin da yake kawo zama masoyi ya danganta da halin mutumin, da yanayin yadda ya fahimci mu'amalar da ka ke yi masa. Wani ya kan so ka ne saboda kyawawan halayenka, wani saboda siffar da Allah ya yi maka, wani kuma kawai gamon jini ne, sai ya ji ka kwanta masa a rai. Wannan shi ya sa maƙiyi na iya juyewa ya zama masoyi, saboda afkuwar ɗaya daga dalilan nan, musamman na ɗaya.


MAƘIYI 

Ƙiyayya na tasowa ne ta dalilin samun saɓani, ko mummunar/kuskuren fahimta, ko saboda waɗansu halayenka da ba su gamsar ba, ko kuma rashin haɗuwar jini. Wannan shi ya sa masoyi kan juye ya zama maƙiyi, domin wani dalili da ya taso daga waɗanda aka lissafa, musamman na 1, na 2 ko na 3.


MAHASSADI

Shi wannan yana faruwa ne sakamakon ɗaukaka ko wata baiwa da ya ga Allah ya yi maka, kamar kyawun halitta, ko ilmi, ko mulki, ko kuɗi, ko ka rabauta da abin da ku ke nema tare, sai shi kuma bai samu ba, ko ya ga mutane suna yaba maka, ko Allah ya ba ka karɓuwa wajen jama'a, ko ki samu mijin aure ita kuma tana kasuwa, da dai abubuwa masu kama da waɗannan. Daga dai zarar ya fara jin cewa shi ne ya fi ka cancanta da duk abubuwan da na zayyana maka.



A kashi na gaba, Insha Allahu, za mu yi bayanin yadda ya kamata ka yi wa kowanne daga cikinsu mu'amala. Idan har matsayinsa ya bayyana gare ka.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user