Sunday, 14 July 2024

Rayuwa Da Abokai (3)

Tura Wannan Zuwa Ga

A kashi na biyu mun yi bayanin dalilan da suke samar da nau'o'in abokan alaƙarka guda uku. Yanzu kuma Insha Allahu, za mu yi bayani a kan yadda ya kamata ka yi wa kowanne daga cikinsu mu'amala, idan har matsayin su ya bayyana a gare ka.


Zama da abokai
Hoto: The tech edvocate


Marubuci:- Abuna'Ila Saminu


MASOYI

Ka riƙe shi kam, ka ci-gaba da yi masa abubuwan da suka sanya soyayyarka a zuciyarsa, ka ƙara fito da sababbin hanyoyin kyautata masa, ka riƙa yi masa kyakkyawar addu'a, da fatan alkhairi a duk wani abin da ya sa a gaba na rayuwa, ka mayar da farin cikinsa naka, haka ma baƙin cikinsa naka.

MAƘIYI

Ka yi ƙoƙarin kawar da saɓani ko rashin fahimtar da ya shiga tsakaninku, ta hanyar nuna masa kyawawan halayenka, ka nuna masa ƙauna da soyayya, ka riƙa shiga sabgoginsa na arziki, da yi masa jajen abu mara kyau da ya faru gare shi, idan kuma na gudunmawa ne ka ba shi iya ikon ka.

MAHASSADI

Ka nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ka taɓa nuna masa cewa ka gano shi, kada ka rika nuna masa duk wata ƙaruwa/ɗaukaka taka, ka toshe masa hanyoyin samun labari game da yadda kake gudanar da rayuwarka, yi ƙoƙarin barin sa a cikin duhu game da hada-hadarka.

Ka riƙa rokon Allah ya yaye masa cutar da ke damun sa, domin ita hassada wata cutar zuciya ce da ba ka da maganinta, sai dai addu'a da neman tsari, duk kyautatawar da za ka yi wa mai yi maka ita, ba za ta taɓa canza zuciyarsa game da kai ba, sai dai kawai ka nemi Allah ya yi maka maganinsa.

KAMMALAWA

Ka sani cewa abokai biyu na iya canzawa, Masoyi da Maƙiyi, amm Mahassadi ba ya canzawa, kuma duk kirkin ka, duk nagartarka, ba ka isa ka ƙetare waɗannan nau'o'in abokan mu'amala guda ukun ba, domin duk abin da kake taƙama da shi na nagarta ba ka kai Manzo (S.A.W) ba, shi ma waɗannan abokan mu'amala ukun da su ya rayu!

Ina ga kuma irinmu 'yan rayuwar ƙarshen zamani ? Allah ka haɗa mu da abokan mu'amala nagari.

Domin samun cikakken bayani a kan hassada, ire-irenta, dalilanta, hukuncinta, hanyoyin rabuwa da ita da sauransu, karanta rubutun da muka yi game da HASSADA a wannan shafin.

'Yan uwa na bar ku lafiya cikin fatan alkhairi mai ɗorewa har abada!

Da fatan Allah ya yafe mana kura-kurenmu!
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user