Friday 5 July 2024

Shawarwari 8 Ga Wanda Yake Son Fara Sana'a Cikin Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Babu shawara ɗaya tilo da za ta biya maka buƙata. Akwai abubuwa da dama da kake nema a lokaci ɗaya da za su kai ka ga nasara idan za ka fara sabuwar sana’a.


Shawarwari 8 Ga Wanda Yake Son Fara Sana'a Cikin Nasara
Hoto: 123RF


MarubuciBello Galadanchi


Ga guda takwas:


1. KA KEƁE KWASTOMOMIN DA KAKE BUƘATA: Ba sai ka ƙirƙiro wani sabon abu ba sannan za ka yi nasara a kasuwanci. Akwai sana’o’i da yawa da za su samu karɓuwa sosai, waɗanda abin da kawai kake buƙata shi ne sana’ar ka ta fi ta ragowa inganci da rahusa. Wata sana’ar kana zaune za ta faɗo maka a rai, amma yadda za ka aiwatar da ita shi ne ta warware wa jama’a matsala ta wata hanya ta daban da ba’a sani ba. Wata sana’ar kuwa sabuwa ce babu wanda ya taɓa yin irinta.


Abu mafi muhimmanci shi ne me za ka kawo mai amfani wanda zai warware wa jama’a matsala kuma kai kaɗai ne za ka iya gudanar da hakan? Shin ka fi kowa ƙwarewa? Ka fi kowa sauri? Ka fi kowa rahusa? Ka fi kowa sauƙin samu? 


Abubuwan da za ka iya yi suna da yawa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne “me yasa kwastomomi za su zaɓi sana’ar ka ba na ragowar masu yin irinta ba?”


Ka tabbatar ka fahimci kishiyoyinka yadda ya kamata, da kuma abubuwan da suka bambanta naka da nasu, sannan ka mayar da hankali akan dalilan da suka sa naka ya fi nasu inganci da amfani. 


2. KOWACE MATSALA TANA DA HANYAR WARWARE TA: Abu ɗaya da duk wani mai fara sana’a yake fuskanta shi ne ƙalubale, kuma ko kana so, ko ba ka so, sai ka samu matsala. Saboda haka idan har za ka fara sana’a ba tare da imanin cewa za ka fuskanci matsala ba, to ka riga ka saka kanka a cikin matsala. 


Amma idan ka saka a zuciyar ka cewa kowace matsala na da hanyar warware ta, to ga matakai na gaba da kake bukata. 


- Ka fahimci ire-iren hanyoyin wareware matsalolin da za ka iya fuskanta.


- Ka auna tasiri da rashin tasirin su.

 

- Sannan ka yanke shawara mafi amfani bisa buƙatar ka. 


Kar ka yi ƙoƙarin wareware matsalar, ka gyara tunaninka sannan matsalolin za su warware kansu da kansu. 


3. BA KAI NE  KA FARA SAMUN WAƊANNAN MATSALOLIN BA: Akwai wanda shi ma ya yi ƙoƙarin wareware su.


Mun yi sa’a, Allah Ya ɗora mu a doron ƙasa, a dai-dai lokacin da sai kana so za ka zauna a cikin jahilci, bisa la’akari da irin ilimi da jama’a suke da shi a duniya. Za ka yi mamakin adadin mutanen da suke da baiwar warware matsaloli a cikin garinku ko ma jiharku. Kar ka yi ƙasa a gwiwa, ka nemi wanda ya fahimci wannan harka, ka yi sauƙin kai, ka nemi shawara. Kar ka ɓata lokaci wajen warware ƙananan matsalolin da akwai wanda ya riga ya warware su. 


4. MUHIMMANCIN FAHIMTAR SHAWARWARIN DA BA ZA SU YI AIKI BA BA ƊAYA BA NE DA WADANDA ZA SU YI AIKI: Idan ka ɗauki lokaci ka nemi ilimi game da sana’ar da kake son farawa, wannan zai rage maka adadin lokacin da za ka ɓata wajen fahimtar shawarwarin da suke da amfani, da waɗanda ba su da amfani. Neman ilimin shi ma zuba jari ne, saboda zai rage maka asara da ɓata lokaci.


Idan har ka ɗauki darussa daga gazawarka kuma a karo na gaba ka yanke shawarwari masu amfani, to za ka ga cewa ka amfana saboda hikimarka da basirarka sun ƙaru, idan aka kwatanta da samun sa’a ba tare da fahimtar dalilin haka ba. 


5. ZA KA YI MARAICI: Akwai ranar da za ka yi tsallen albarka ka miƙe tsaye domin fara sana’arka. Amma ka san da sanin cewa wannan sana’ar taka ce kai kaɗai, kuma ba lallai ba ne ragowar jama’a su fahimci hangen nesan ka, da irin burinka. Kar gwiwar ka ta yi sanyi saboda ba ka samu damar fara sana’ar ba. Kar ka yi waswasi, kuma kar ka ja da baya. Kar ba bari wani abu ya kashe maka burinka.


Ka dage akan cewa sai ka fara wannan sana’a da ikon Allah, sannan duk ranar da ka yi nasara, to jama’a za su zama masu bada labarin yadda ka fara daga farko har ka kai ga nasara. 


6. IDAN BABU WAHALA, TO BA KA AIKI TUƘURU: Da akwai sauƙi, to da wani ya riga ka yi. Haka duniyar nan take. Fara sana’a na da matuƙar wahala, kuma sana’ar da za ka samu arziki ta fi wahalar gudanarwa. Idan har abubuwa suka yi wahala, to sai namijin duniya ne yake ci-gaba da gashi.


Idan ba ka da taurin zuciya da ƙarfin halin yaƙi da ƙalubalen sana’arka, to ba za ka samu wani abun a zo a gani ba. Sai dai duk ƙalubalen da ka warware, to hakan zai ƙara maka ilimi da karfin gwiwa da hikimar warware matsalolin da za ka fuskanta a gaba cikin sauƙi.


7. ƘANANAN NASARORI SUN FI MANYA MUHIMMANCI: A yunƙurinka na cimma burinka na rayuwa, tuƙa mota mai kyau da mallakar gidan kanka wata ƙila su ne ma’anar nasara a zuciyarka. Amma akwai matuƙar muhimmanci ka godewa Allah (S.W.T) ga duk wata ‘yar ƙaramar nasara da ka samu. Wannan ne zai ƙara maka ƙarfin gwiwa, kuma Allah zai ƙara buɗe maka hanyoyi wajen gina sana’arka har ka kai ga nasara. Ba kowa ba ne yake yin sa’a tashi ɗaya, saboda haka dole sai ka kimtsa zuciyarka da imanin cewa juriya, haƙuri da jajircewa su ne motocin da za su tuƙa sana’arka akan titin rayuwa har ka isa garin nasara. Masu azancin magana suka ce “da rarrafe……”. 


8. IDAN KA MANTA DA JAMA’A, TO KA MANTA DA RIBA: Kusan kowa yana sana’a ne domin ya samu riba. Amma duk da haka, kar ka taɓa mantawa cewa babu abin da za ka iya yi sai da jama’a. Mutane su ne komai. Mutane ne kwastomominka, mutane ne ma’aikatanka, kuma mutane ne dilolinka. Idan ka kyautata kuma ka mutunta mutane, ko su waye, kuma ko a ina suke, kuma a kowane hali suke ciki, to sana’arka za ta shiga sahun sana’a’o’i masu albarka. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user