Assalamu Alaikum Warahmatullah. Bayan Shimfiɗaɗɗiyar sallama wacce addinina ya tanadar, ya harkokin yau da kullum? Ya lafiyar ka? Bayan haka kada ka yi mamakin ganin wannan wasiƙa tawa ko kuma Shaiɗan ya yaudareka cewa kada ka amince da ni domin na yi tallar kaina a gare ka.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Sam-Sam kada ka yarda da hakan, domin ya zo a hadisan Manzon Allah (S.A.W) cewa a zamaninsa an samu mata suna zuwa ga maza suna neman amincewarsu domin su yi aure.
Don haka neman soyayyar namiji a wajen mace ba rashin aji ba ne ko zubar da kima.
Wannan shi ne cikakken aji da kyautatawa domin mun yi koyi da bayin Allah na ƙwarai.
Sunana zuciya ta unguwar ƙauna, wataƙila ka san ni, wata ƙila kuma ba ka san ni ba.
Watarana ina tafiya na haɗu da kai a hanya, cikin ikon Allah sai na ji na kamu da soyayyar ka sakamakon ganin kamalarka, ilimin ka, hankalinka, iya adon ka da sauransu, zuciyata ta aminta da kai, ta fara azabtar da gangar jikina.
Lallai ina buƙatar agaji daga gare ka, don haka zan so ka ziyarce ni ta hanyar adireshina.
Kamar haka: Gida mai lamba 143 unguwar ƙauna jihar soyayya, wata ƙila idan ka gan ni ka aminta da ni.
Idan ma ba ka aminta da ni ba, ka amince na yi tarayya da kai, na san a hankali wani yanayin nawa zai iya fizgar zuciyar ka zuwa ga sona kamar yadda halayen ka suka fizgi tawa zuwa ga son ka.
Ina nan ina jiran ka a kowanne hali.