Wani Magidanci ne yana zaune da matarsa suna hira sai ta ce "Bari na kawo maka abinci ka ci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa".
Sai ya ce "To Uwargida me aka dafa ne yau?".
Sai ta ce "Shinkafa da miya".
Sai ya ce "Ina fatan dai ba a gidan maƙwabcinmu kika sayo tumatur ɗin ba ko?"
Sai ta ce "Kamar ka sani a can na sayo, kenan ya ya zan yi?"
Sai ya ce "Ina tsoron ko ya saka guba ne a cikin tumatur ɗin".
Sai ta ce "Ai sai da na fara bai wa karen gidan nan tukunna kafin na kawo maka Maigidana".
Sai ya ce "To shikenan". Ya fara cin abincin kenan, sai 'yar aikin gidan ta shigo ta yi sallama ta ce "Alhaji Maigadi ya ce na gaya maka karen gidan nan ya mutu".
Nan take Alhaji ya karaya sai ya cewa matar tasa "Kafin na mutu zan roƙi gafarar ki domin na yi miki laifi. Mun haifi yara biyu da 'yar aikin gidan nan.".
Sai matar ta ce "Ni ma ka yi mini afuwa a cikin yaranka guda shida, huɗu na Maigadi ne biyu ne kawai naka.".
Ana haka sai Maigadi ya shigo, ya ce "Alhaji wani ne ya yi sallama yanzu koda na amsa sai yake gaya min cewa, a ba ka haƙuri shi ne ya buge karen nan da mota har ya mutu".
Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba.