Wani manomi ne dai ya ke da jakinsa wanda ya ke aiki da shi shekara da shekaru. A kwana a tashi jaki ya fara tsufa har ba ya iya moriyar maigidansa da komai. Da manomi ya ga haka sai ya fara shawarar yadda zai rabu da jaki ko ma ya halaka shi ya huta da ciyar da shi da ya ke yi kullum.
Marubuci: Bukar Mada
Da jaki ya gane abin da manomi ke shirin ƙulla masa sai ya gudu. Ya ce a ransa, "Bari na shiga birni na koyi waƙa, wata ƙila na zamo mai dogaro da kaina!"
Yana cikin tafiya a hanya, sai ya haɗu da kare yana kwance a gefen hanya, sai faman fuka ya ke yi. Jaki ya tambayi kare me ya same shi ya ke ta fuka?
Kare ya ce, "Ai da ƙyar na sha a hannun mai gidana, wai zai kashe ni saboda yanzu na tsufa ba na iya farauto masa komai. Yanzu ina tunanin yadda zan yi da rayuwata in riƙa samun abinci"
Jaki ya ce, "Af! Matsalarmu ɗaya da kai. Ni zan shiga birni ne na koyi waƙa, idan za ka bi ni taso mu je." Kare ya tashi ya bi Jaki suka ci gaba da tafiya.
Ba su yi nisa da tafiya ba, sai suka haɗu da kyanwa/mage a kan hanya, tana tafiya shajaran majaran, kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwan zafi.
Jaki ya dube ta ya ce, "Ah, su maguru 'yan gatan mutane, yau kuma me ya same ki duk kamarki ta canja haka?"
Kyanwa ta dubi Jaki ta ce, "Ba dole kamata ta canza ba, uwargijiyata na neman ta halaka ni wai saboda na tsufa, ba na iya kama ɓerayen da suke yi mata ɓarna a gida. Sai dai na sha madara na kwanta a kan shimfiɗa ina lashe jikina. Wai ita ta gaji da ba ni madara tunda ba ni da moriyar komai. Yanzu ban san yaya zan yi da rayuwata ba."
Jaki ya ce, "Kai 'yan Adam akwai butulci, mu ma abinda ya faru da mu ke nan. Za mu shiga birni mu koyi waƙa, mu dogara da kanmu, idan za ki bi mu shi ke nan." Kyanwa ta amince da bin su.
Jaki da kare da kyanwa suka kama hanya suka nufi birni. Suna cikin tafiya sai suka haɗu da zakara, gashin jikinsa a yamutse. Jaki ya tambaye shi abin da ya same shi.
Zakara ya ce, "Na yi daron yanka ne! Yau ina cikin hutawa sai na ji maigidana ya kama ni, wai zai yanka wa baƙonsa da zai kawo masa ziyara, ni kuwa ban san lokacin da na fizge daga hannunsa ba. Ina cikin gudu ke nan muka haɗu da ku."
Jaki ya ce, "Mu ma nan duk guduwa muka yi daga iyayen gijinmu. Za mu shiga birni ne mu koyi waƙa, idan kana da sha'awa ka biyo mu mu tafi. Zakara ya bi su, suka rangada.
Can sun kusa isa birni sai dare ya yi musu. Jaki ya ce su kwana a nan kafin gari ya waye su shiga birni. Suka sami wata babbar itaciya, Jaki da Kare suka kwanta a ƙarƙashin ta, Kyanwa da Zakara kuwa suka hau saman itaciyar. Zakara ya haye can ƙololuwar itaciya.
Da dare ya fara yi sosai, sai Zakara ya ƙyalla ido ya hango hasken wuta can nesa da su. Ya faɗa wa saura, suka ce lalle gida ne inda hasken nan ke fitowa, yana da kyau su matsa can su kwana, da su kwana cikin daji. Suka tashi suka nufi inda hasken ke fitowa har suka zo dab da shi. Suka ga ashe gida ne, kaɗe-kaɗe da bushe-bushe na fitowa daga ciki.
Suka matsa kusa da wani ɗaki da tagarsa take a buɗe. Da ya ke Jaki ya fi su tsawo, sai ya leƙa ta tagar. Ya ga mutane ne zaune, suna ci suna sha, wasu kuma suna kiɗa da busa da rawa. Jaki ya faɗa wa abokan tafiyarsa abin da ya gani. Ya tambaye su ko akwai dabarar da za su yi su kori mutanen nan su mallake gidan, su yi zamansu a nan suna koyon waƙa.
Kare ya ba da shawara cewa, zai hau bayan Jaki, kyanwa ta hau bayansa, Zakara ya hau bayan Kyanwa, su afka cikin ɗakin, mutanen za su ji tsoro su gudu su bar musu gidan. Duk suka amince da wannan shawara ta kare.
Kare ya hau bayan Jaki, kyanwa ta hau bayan Kare, Zakara ya hau bayan Kyanwa. Suka shiga gidan, suka zagaya ta ƙofar ɗakin, suka afka cikin ɗakin. Jaki ya ƙwala kuka, kare ya yi haushi, kyanwa ta yi kuka, zakara ya ƙwala cara. Mutane suka firgita, suka yi waje da gudu, suka bar kayan kiɗa da busa.
Jaki, kare, kyanwa da zakara suka zauna suka ci suka sha, suka yi hani'an. Sun samu gida, ga kuma kayan waƙa sun samu. Da suka gama cin abinci, suka kwanta domin su huta, zuwa da safe su fara koyon waƙarsu.
Mutanen nan kuwa da aka kora daga cikin gida, suka yi ta mamakin abin da ya koro su daga cikin gidan nan. Can suna tsaye suna hangen gidan daga nesa, sai suka ga an kashe wutar gidan, ya koma cikin duhu. Sai wani mutum mai ƙarfin hali da jarumta a cikinsu ya ce zai je ya dubo ko mene ne a cikin gidan nan.
Ya tafi har ya shiga cikin gidan, ya shiga cikin ɗaki. Ya laluba inda ashana ta ke ya ɗauka. Ya ƙyasta domin ya kunna fitila, sai kuwa hasken ashanar nan ya ɗauko idanun kyanwa, ya gansu war war war. Sai ya tsorata ya yi waje da gudu, wajen fita ya taka wutsiyar kare, da kare ya ji zafi sai ya zafga masa cizo a ƙafa har jini ya fita. Ya ƙara ruɗewa ya faɗa wa jaki. Jaki kuma ya taƙarƙare iya ƙarfinsa ya watsa masa harbi, ji kake tim!
Mutumin dai ya yi ƙarfin hali ya fita da gudu. Kafin ya fita kuma zakara ya yi tsalle ya karta masa yaga a fuska. Yana isa wurin 'yan uwansa, sai ya ce musu ai sarkin aljanu ne ya sauka gidan da rundunarsa gaba ɗaya, akwai masu wuƙaƙe, akwai kuma masu kulake, don haka kada wanda ya kuskura ya ƙara zuwa kusa da gidan nan.
Jaki da kare da kyanwa da zakara suka yi zamansu cikin gidan nan, ga abinci da ruwa, ga kuma kayan kiɗa da busa. Suka yi ta koyon waƙarsu, ba wani mutumin da ya ƙara kuskura ya matsa kusa da gidan nan, ballantana a dame su. Wa ma zai matsa kusa da fadar sarkin aljanu ya sha kulake!
Kurungus kan ɗan ɓera, ba don gizo ba, da na yi ƙarya....!