Mataki na farko shi ne yanke shawara a kan wacce irin sana’a kake so ka yi, sannan ƙalubale na gaba shi ne samun jari. Wasu sana’o’in ba sa buƙatar ƙaton jari, sannan wasu ƙalilan za’a iya fara su ba tare da jari ba amma da yawansu na buƙatar jari mai tsoka, kuma mafi yawancin waɗannan ‘yan kasuwan na buƙatar tallafin bashi a lokutan da suke ƙoƙarin bunƙasa domin ci-gaba.
Marubuci: Bello Galadanchi
Dolen dole sai mai sha’awar fara sana’a ya shawo kan masu zuba jari, kuma ya tabbatar musu cewa sana’ar za ta yiwu, kuma yana da ƙwarewa da ilimin aiwatar da wannan shawara wajen ganin ta zama sana’a mai nasara da bunƙasa.
Babban abun la’akari shi ne ko sana’a tana kawo riba ko saɓanin haka. Akwai lokuta da dama da idan ka saurari shawarar sana’a, ko ka karanta ta akan takarda za ka ga ta burge ka, amma idan aka aiwatar da ita, sai ka ga babu komai a cikin ta. Saboda haka, akwai matuƙar muhimmanci ka nazarci kishiyoyinka a wannan sana’a, da kuma kwastomominka kafin ka tantance ko sana’ar za ta kai labari.
Ga abubuwan da za ka iya bincikawa:
Wane ne yake gasa da kai wajen jawo hankula da kuɗaɗen kwastomomi? Shin wanne irin kallo ake wa kishiyoyinka a kasuwa? Mene ne girman kasuwar?
Samun tagomashi a kasuwanci ya dogara ne akan abubuwa biyu. Na farko shi ne ka zama na farko wajen kawo wannan kaya ko sana’a, ko kuma ka bambance kanka sosai daga kishiyoyi. Misali shi ne shafin saye da sayarwa mai suna “ebay” shi ne na farko a irinsa akan yanar gizo, kuma tun 1995 har zuwa yau, shi ne sarki . Haka zalika kamfanin ƙirar mota na “Volvo” shi ne ya fara ƙirƙirar manyan motocin bus na nishaɗi a ƙasar Indiya, kuma tun wannan lokaci yake samun ciniki mai tsoka. A ɗaya ɓangaren kuwa, shafin sada zumunci na “facebook” ba shi ne na farko ba a shafukan sada zumunci, amma an fi amfani da shi saboda ya fi ragowar daɗin amfani.
A ƙarshe, da zarar ka fara sana’a, to ƙalubale ya koma kan yadda za ka bunƙasa ciniki. Allah Ya taimaka.