Sunday 11 August 2024

Hanyoyi 10 Na Gane Masoyan Gaskiya Da Munafukan Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

Muddin namiji ko mace ba za su iya bambance tsakanin masoya na gaskiya da na ƙarya ba, a kullum za su riƙa faɗawa cikin matsaloli na soyayya.


Gane Masoyan Gaskiya Da Munafukan Masoya
Hoto: Medium

Marubuci: Mahadi Idris Matawalle


Ga wasu hanyoyin da maza da mata za su iya bambance masoya na gaskiya da na ƙarya. 


Duk da darasin ya fi karkata ne ga mata, amma akwai wasu alamomin da maza ma za su iya amfani da su.


1. Masoyi na gaskiya yana iya yin komai a kanki domin ganin ya biya miki buƙatar ki amma shi mai soyayya na ƙarya kansa kawai ya sani. 


Duk wani abu na matsala idan ya taso ba za a gan shi ba sai abin ya wuce.


2. Shi mai son ki da gaske ba zai taɓa furta miki kalamai na ƙarya ko na yaudara ba koda wasa ne, amma shi maƙaryacin masoyi bai da abin faɗi sai na ƙarya da yaudara.


3. Duk wani mai son ki na gaskiya zai riƙa tausaya miki, amma shi maƙaryacin masoyi bai da wani aiki sai gallaza miki da ƙuntata miki.


4. Duk wani mai son ka za ka same shi yana da haƙuri kuma yana maka uzuri, amma shi maƙaryacin masoyi komai nasa na fushi ne da ɓata rai da son a yi faɗa.


5. Idan namiji na son ki kwantar da kansa ƙasa yake komai matsayinsa da girmansa, amma shi maƙaryacin masoyi gadara, taƙama da nuna miki isa su ne ɗabi'u sa.


6. Ita macen da take son namiji da gaske za ka same ta da yaba kyauta komai ƙanƙantar ta, amma macen da son ƙarya take maka, duk abin da za ka mata sai ta raina ga rashin godiya.


7. Idan namiji na son ki da gaske zai riƙa girmamaki da mutunta ki, amma shi masoyin ƙarya ba ya ganin darajar ki da mutunci a sarari da ɓoye.


8. Idan ana maka so na gaskiya za a yi ƙoƙarin kare mutuncinka ne a duk inda ya kama, amma idan soyayyar ƙarya ce su ne ma za su so ma jawo zancen da za a ci maka mutuncin.


9. Idan mace tana maka so na gaskiya cikin ƙaramin lokaci za ta yi ƙoƙarin ganin ta fahimce ka amma ita wacce ba ta maka so na gaskiya ko lambar wayarka ba za ta iya kawowa a kanta ba bare ta fahimci wasu halayen ka.


10. Duk wani mai son ki na gaskiya ba zai taɓa nuna miki rashin yarda ba ko zargin ki amma namijin da ke miki ƙaryar so a kullum cikin rashin yarda da ke yake saboda yawan zargin ki.

 

Waɗannan wasu ne daga cikin alamomin da mata da maza da suke soyayya za su iya tantance mai so na gaskiya da na ƙarya, haka nan masu son ka a zahiri na rayuwa da masu cewa suna son ka a baka.


Allah Ya sada mu da masu son mu na gaskiya Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user