Domin iya rayuwa mai kyau a Najeriya sai kun koyi waɗannan abubuwan guda goma.
Marubuci:- Khalid A Gombe
1. Bajet: ka dinga ware nawa za ka dinga kashewa a wata ko sati, hakan zai sa ka dinga lura ba za ka dinga kashe-kashe kana rasa inda kuɗin su ke zuwa ba. Sannan zai sa kuɗi ba zai dinga yanke maka kafin ka samu wani ba.
2. Ka hau motar haya: idan kana da abin hawa, ka dinga ajiyewa sai lokaci zuwa lokaci. Ba kowace rana ce za ka hau motarka ko mashin ɗinka ka je inda akwai ababen hawa na haya suna zuwa ba. Ka tuna cewa koda za ka iya siyan fetur, yawan hawa abin hawanka zai ɓallo maka gyara kuma za ka dinga yi masa juyen baƙin mai.
3. Gyara Tauhidinka: yana da kyau ka sani sai ka yi aiki Allah zai ba ka. Kada ka kwanta a ɗaki ko ka dinga bacci kana zaton ai an ƙaddara maka kuɗi ko talauci. Allah ya yi alƙawarin idan ka yi ƙoƙari to zai ba ka, ko Annabawa sun yi sana'a. Don haka ka fara tashi tsaye sai kuma ka roƙi taimakon Allah.
4. Rage yawaitar biki: Ka rage kashe kuɗi a kan biki irin na su tunawa da ranar haihuwa (Birthday) ko na bikin shekara don tunawa da wani abu (Anniversary) ko kuma na taron buki (Wedding) mai tsada. Irin waɗannan abubuwan suna cinye kuɗi ba tare da ka ga manufarsu a zahiri ba. Maimakon haka, ka zuba kuɗin wajen gina rayuwarka kamar siyan fili don gini ko kuma kasuwanci.
5. Gayawa kanka gaskiya: ya kamata ka san kai talaka ne. Ka gaya wa kanka gaskiya kai fa talaka ne. Ka daina ƙoƙarin yin abin da zai nuna kai mai kuɗi ne a idon jama'a alhalin a zuciyarka ka san ba ka da kuɗi.
Abubuwa irin su ɗinke-ɗinke, siyan takalma da huluna masu tsada suna da lokacinsu. Kai talaka ne don haka ka gane lokacinka bai zo ba.
6. Ka rage kashe kuɗi a "subscriptions": yawan hawa TikTok yana zuƙe Data. Yawan hawa YouTube yana zuƙe Data. Don haka ka sani cewa kuɗinka mai yawa yana tafiya a data, don haka sai ka saita rayuwarka. Idan kana da subscriptions da Netflix, to ku haɗa kuɗi ku huɗu ko biyar ku dinga biya tare maimakon kai kaɗai.
7. Wutar lantarki na shirin ƙara tsada a Najeriya kuma za a raba mitoci a gidaje a unguwanni da lunguna. Idan har mita ta zo maka to ka dinga kula wajen kunna kayan wuta. Ka rage kunna AC a ɗakin da ba kowa. Ka siyo kayan wuta marasa zuƙar wuta da yawa, sannan ka dinga kashe ƙwan fitila idan ka fita daga ɗaki.
8. Rage cin bashi: ka daina cin bashin banki idan ka san ba kasuwanci za ka yi da kuɗin ba. Kada ka ci bashin gwamnati ka yi aure. Kada ka ci bashin kamfanoni ka sayi waya. Ka daina cin bashi da yawa. Ka daina kai kanka inda ba ka kai ba.
9. Ka koyi ƙananun gyara: ka koyi saita kwanon tauraron Ɗan Adam (Satellite) ɗinka. Ka koyi gyaran soket (Socket) ɗin gidanka. Ka iya gyaran famfon gidanka da kanka. Ka koyi zuwa aike ba tare da ka nemo ɗan aiki ba. Ka koyi sauran ƙananun gyararrarki ba tare da sai ka ɗauko wani ya yi maka ba.
10. Ka yi aiki tuƙuru. Ka yi aiki tuƙuru. Ka yi aiki tuƙuru. Sannan ka yi addu'a. Manyan abubuwa kamar gina gida ko siyan mota sun fi zuwar wa mai aiki tuƙuru. Idan ba haka ba sai dai kawai ka ga ana yi amma kai ba za ka samu ba. Ka buɗe hanyoyin samunka. Hanya ɗaya ba za ta ɓulle ba. Idan da dama ka yi ayyuka masu yawa don faɗaɗa samunka. Ka zama mai sana'a goma ka magance talauci.