Bello Habib Galadanchi wanda aka fi sani da Bello Galadanchi ko Ɗan Bello Ɗan wasan barkwanci ne, sannan marubuci ne, sannan Ɗan Kasuwa ne. Sannan kuma yana shiryawa tare da bayar da umarni a fina-finai. Ya kuma kasance Ɗan Jarida ne shi.
Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.
Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nasa.
Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:
Ɗan Bello ya yi karatun firamare a Al-Iman School Jos, ya yi makarantar sakandare a Ulul Albab Science Secondary School Katsina, sannan ya yi digirin ɗin shi na farko a jami’ar Pennsylvania da ke ƙasar Amurka. Sannan kuma ya yi karatun MBA da PhD a ƙasar sin (China).
Ya yi aiki a sashin watsa shirye-shirye na harshen Hausa da kafar watsa labarai ta ƙasar Amurka wadda aka fi sani da Muryar Amurka ko VOA. Ya kuma yi aiki da kafar watsa labarai ta Birtaniya wato BBC.
Shi ne kuma wanda ya samar da Kasuwar Bello, wadda ake tafiyar da harkokin ta anan shafukan yanar gizo-gizo.
Yanzu haka yana gudanar da binciken kimiyyar ilimi a ƙasar Sin.
Yana kuma koyarwa a irin makarantun Yara, haka kuma yana koyarwa a fannin kasuwanci da harshen chainanci, har yau kuma ya kasance shugaban malamai na ƙasashen waje na ƙasar Sin. Idan ku ci gaba da bibiyar mu, nan gaba kaɗan za mu kawo muku tarihin yadda ya fara koyarwa a ƙasar Sin ɗin.
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe domin samun asalin cikakken tarihin Bello Galadanchi wato tarihin Dan Bello tare da zafafan hotunan shi na musamman.