Daga cikin raminsa, ɗan ɓeran na kallon sa'adda maigida ke ta cuku-cukun haɗa masa tarko. Da ya gama sai ɓera ya fito ya nufi wajen zakara a firgice ya ce, "abokina ka taimake ni, an sa mini tarko a gidan nan."
Marubuci: Bukar Mada
Zakara ya kaɗa fiffike yai shewa ya ce, "ina ruwan maza da wankan jego? Me ya sha mini kai da tarkon da aka sa maka, ɓarnarka ce ta jawo maka."
Ɓera ya wuce wurin zomo ransa a ɓace ya ce, "ɗan uwana ka taimake ni, an ɗana mini tarko a gidan nan."
Zomo ya harare shi ya ce, "wane ne ɗan uwan naka? Kai dai nemi su jaɓa da gafiya."
Ɓera ya ce, "ko da ba jinsinmu ɗaya ba, ai dukkanmu dabbobi ne, ya kamata mu haɗa kai mu tunkari matsalar da ta doso ɗaya daga cikinmu."
Zomo ya ce, "wuce ka ba ni wuri! Maganinka ke nan ai, ɓuruntunka ne ya jawo. Idan jifa ta wuce kaina, to ta faɗa kan kowa ma."
Cikin takaici ɓera ya nufi wajen rago ya ce masa, "ɗan uwa ka taimake ni, an haƙa mini tarko."
Rago ya yi dariya ya ce, "af, to me ya haɗa kifi da kaska kuma? Kai, ni raba ni da zancen kawai, in ka ƙi ko yanzu ina murje ka! Tafi ba ni wuri."
Ɗan ɓeran nan ya koma cikin raminsa cike da taikaicin yadda sauran dabbobi suka baɗa masa ƙasa a ido.
Can cikin dare sai aka ji kararaf! Tarko ya kama.
Ɗan maigidan ya zabura da sauri ya fita don ya cire gawar ɓera daga tarkon. Ashe maciji ne ya jefa wutsiyarsa ciki. Yaro na zuwa maciji ya sare shi, aka ɗauke shi kamar tsumma sai asibiti. Ɗan nan kuwa shi ke nan, ƙwallin ƙwal, ga uban.
Da safiya ta yi, maigida ya sa aka kama zakara aka yi wa yaro dabge/farfesu/dage-dage.
Bayan kwana biyu kuma aka yi farfesun zomo, aka kai wa yaro ya sha lagwada.
Da aka sallami yaro daga asibiti, saboda farin ciki, uban ya sa aka murƙushe rago aka yanka, aka yi abinci aka raba wa maƙota sadaka.
Duk wannan kicimilli da aka yi a gidan, ɗan ɓeran nan na cikin raminsa kwance yana kallon ikon Allah. Ya ce a ransa, 'da sun taimake ni mun kawar da tarkon, da abin da ya faru duka bai faru ba. Matsalar da ta doshi ɗaya, za ta iya game duka.'