Sunday, 25 August 2024

Karanta Kalaman Barka Da Safiya Na Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

Amincin Allah da rahamar Sa da albarkar Sa su ƙara tabbata a gare ki yake abar ƙauna, fitila mai haska duhun da ke cikin rayuwata.


Kalaman Barka Da Safiya Na Masoya
Hoto: Pixabay


Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Karya Kumallo/Karyawa/Karin Kumallo (Break fast)  mafi armashi da gamsarwa a gare ni shi ne cikin sanyin safiyar da na farka a bacci kunnuwana su fara da sauraron zazzaƙar sautin tatacciyar muryar ki wacce zaƙinta ya fi na sarewa wane garaya ko idanuwana su yi tozali da haɗaɗɗiyar fuskar ki wacce ta fi wa idanuwa daɗin kallo fiye da komai a duniya.


Da ma a ce ina kusa da ke da na sanya ruhina cikin aminci da daddaɗan yanayi ta hanyar yawan kusantar ki, musamman a lokacin da kike farin ciki da annushuwa.


Barka da safiya sarauniya mamallakiyar masarautun biranen zuciyata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user