Friday, 30 August 2024

Karanta Kirarin Masoyiya Mai Ratsa Zuciya

Tura Wannan Zuwa Ga

Na gaishe da sarauniyar kyawawan duniya.


Ma'abociyar yalwatacciyar kyakkyawar fuska.


Mamallakiyar haskakakken fararen idanuwa.


Kirarin Masoyiya Mai Ratsa Zuciya
Hoto: Freepik

MarubuciImran Musa Jahun

Sannu, sannun ki gimbiya mai tsararriyar halitta mai kyau da diri.


Takawar ki lafiya ƙasaitacciya, ɗawisu kike mai tafiyar ƙasaita.


Zarah kike mai haske na sirri.


Na gaida ma'abociyar iya lumshe idanuwa.


Dukkan kuyangin 'yammata a bayan ki suke, sahiba ta masoyiyata.


Na gaida ke zinariya.


Zabiya kike mai siririyar zazzaƙar murya.


Ba su kai ba, kuma sun gaza kamo ki.


Ke ce kaɗai tilo mai haske gani na.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user