Saturday, 17 August 2024

Karanta Sabon Kalaman Soyayya Mai Dadi

Tura Wannan Zuwa Ga

Daga yanzu har zuwa rayuwar da zan yi a gaba, zuciyata za ta ci gaba da bibiyarki cikin soyayya da ƙauna tsantsa.


Sabon kalaman soyayya
Hoto: Tripadvisor

Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Tukwicin soyayyata a gare ki shi ne tsantsar kulawa tare da tarairaya a zaman da zan yi tare da ke. 


Zan nisanta ki daga dukkan damuwa tare da kusanto miki da farin ciki a zuciyarki.


Soyayyar ki tamkar wani sihiri ne da ya shiga zuciyata, a kullum da koyaushe ina jin motsinta a jikina, a duk wani giftawar lokaci ji nake tana ƙara girmama a gare ni.


Kasancewa da ke shi ne fatana na ƙarshe a cikin jerin burikana. Zan so cikar shi domin hakan ne tabbatar farin cikina a soyayya.


Ke farar zinariya ce wadda ta ke haskakawa a tsakanin dare da rana. Idanuwana a duk yayin ganinki haka suke gani a tare da ke, ta tabbata ke ta daban ce a gare ni.


Kina da tsantsar kyau wanda ba na ganin irin shi a tattare da dukkan sauran 'yammata. Ke ce ƙarshen maƙurar kyawun ganina wanda kin rasa ta biyu a gare ni.


Ina jin cewa na gama samun wacce ta dace cikin 'yanmata.


Zan yi farin ciki da samunki a rayuwata, ba zan yi nadama ba, har abada da ke nake son rayuwa. Ina son ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user