Masu ƙago shubuhohi da yaɗa su sukan ɗaure su a wasu turaku domin nuna cewa su ma suna da hujjoji da dalilai a kan abubuwan da suke faɗa.
Marubuci: Ahmad Murtala Mansur
Manyan turakun shubuhohi su ne:
1. Murguɗa ma'anar ayoyin Alƙur'ani da canja musu fassara idan sun saɓawa ra'ayin su.
Sau da yawa sukan fake da cewa ba zai yiwu a kafa hujja da zahirin aya ba , sai dai a yi mata Tawili . Sukan fake da amafani da kalmar Majazi (مجاز) musamman kan ayoyin siffofin Allah Ta'ala.
2. Ƙaryata ingantattun hadisai da yi musu mummunar fassara ta son rai wacce take cike da ɓatanci ga Allah Ta'ala ko Manzon sa ko Alƙur'ani ko Musulunci. Sai kuma su ƙagawa Sahabbai da Malaman musulunci wannan fassarar.
3. Kafa hujja da hadisan ƙarya da ruɓaɓɓun ruwayoyin tarihi, alhali ga sahihan hadisai da babu wani rikici a cikin su, amma sai su yi fatali da su su maƙalƙalewa waɗannan ruɓaɓɓun.
4. Cushe a cikin ruwayoyin hadisai da na tarihi, sai su cusa wata kalma ko jumla a cikin ruwayar domin cim ma mummunar manufar su ta kawo ruɗani ga musulmi.
5. Rusawa babu ginawa. Aikin masu ƙago shubuhohi a kodayaushe shi ne su rusa tabbatattun abubuwa na musulunci ba su gina ba.
Za su kawo rikici amma ba za su kawo hanyoyin warware shi ba.
6. Kafa hujja da maganganun kafirai da sauran ɓatattu fanɗararru da goya musu baya.
7. Cika baki da kuri da da'awar ilimi, da yi wa Malamai ba'a da izgilanci da nunawa mutane cewa su malaman jahilai ne.
8. Kambama al'amura da zugwigwita su da tayar da ƙura da mayar da allura ta zama garma, da yawan surutu da sunan karatu, duk don su jawo hankalin mutane su saurare su kuma su yarda da su.
9. Tawaye da tsageranci ga magabata matattu da rayayyu da nuna su a matsayin daƙiƙai , jahilai, maha'inta, gidadawa , maƙaryata da sauran miyagun siffofi domin su raba su da mutane su zama ba sa sauraron kowa sai su kaɗai.
Da tsaurin ido da cin mutuncin duk wanda ya saɓa musu koda kuwa ya wuce shekaru dubu da mutuwa.
10. Da'awar jaddada addini da ba shi kariya da tsaftace shi da kuma zamanantar da shi.
A kan haka suke cewa wai su kare martabar Manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da Muslunci suke yi.
11. Da'awar jarumta da nuna su ba sa tsoron kowa kuma wai su don Allah suke yin abin da suke yi ba neman suna ko muƙami ko wani abin duniya suke ba.
Da waɗannan turaku da makamantan su masu yaɗa shubuhohi suke amfani domin ɗaure mabiya da kifa musu kwando su yi ta bin su a makance suna yi musu tafi da jinjina da maimaita waɗannan shubuhohin nasu kamar 'yan amshin Shata.