Shin ko kin san yadda ya kamata ki tarbi masoyinki kuwa a lokacin da ya zo wajenki zance? Duk da kin sani akwai buƙatar ki san da cewa da farko kamar yadda kika sani ne, akwai buƙatar ki ɓata lokaci a gaban madubi wajen yi wa saurayinki da kike so kwalliya ta musamman, a dukkan lokacin da ya shirya kawo miki ziyara.
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
Ki zaɓo kaya masu kyau daga cikin kayanki ki yi masa ado da su. Ki kasance mai sanya kayan da za su rufe miki jikinki su fito da ke a macen da ta san abin da take yi kamar yadda na san kin riga kin san da wannan tini, hakan zai sa ki yi kwarjini a cikin idanuwansa.
Bayan kin futo wajensa, tattausan murmushi shi ne abun da za ki fara jifansa da shi, bayan nan sai ki yi masa sallama tare da yi masa barka da zuwa.
Ki kasance mai ƙawata muryarki a yayin da kuke hira, wato ki yi masa magana cikin nutsuwa da kuma furta masa zaɓaɓɓun kalmomi daga cikin bakinki.
Ki kasance mai mayar masa da amsoshin maganganunsa cikin salo na burgewa kar da ki yawaita ce masa "E, a'a."
Kar da ki yawaita yin maganganu mara ma'ana a gabansa, ki kame kanki cikin salo na jan-aji.
Kar da ki nuna ƙosawa da jin abun da yake faɗa ko hirar da yake yi miki, a lokacin da kuke tare.
Idan lokacin da kike son komawa gida ya yi, shi kuma a daidai wannan lokacin sai ya kasance ya na jin daɗin hirar da kuke yi, sai ki sanar da shi kina son za ki koma gida cikin nuna yanayin ba ki so faruwar hakan ba, wato ba ki so rabuwar taku ba a daidai wannan lokaci, har ki ba shi haƙuri gami da sanar da shi za ki kasance cikin kewarsa har zuwa ranar da za ku sake haɗuwa ko ma shi ya ce zai tafi to ki nuna ba ki ji daɗin rabuwar taku ba a daidai wannan lokacin.
Hakan zai ƙara bayyanar masa da adadin yadda kika damu da shi.
Kar da ki buɗe wa saurayi ƙofar da zai raina ki, ya daina ganin girmanki da kimarki har yake nuna ai ke kike son shi, ba shi ne yake son ki ba, ta hanyar nuna masa azababbiyar soyayya fiye da yanda yake nuna miki domin hakan zai iya sanyawa ya rage kulawar da yake ba ki, yana mai fariya da ai ba za ki iya rabuwa da shi ba.
A dai lokacin da kuke tare, kar da ki manta da yi masa tattausan murmushi, domin kuwa shi zai ke gani a duk lokacin da ya rintse idanuwansa bayan kun nesanta da juna.
Kar da ki manta da ƙawata muryarki wadda gwalagwalan kalmomi za su ke futa daga cikin ta, domin kuwa ita ce sautin da zai fi maimaituwa a cikin ƙwaƙwalwarsa a dukkan lokacin da zanen kyakkyawar taswirar surarki da ya gan ta cikin ƙawatacciyar kwalliyarki ta bayyana a cikin tunaninsa.
Kar da ki kasance mai yi masa kowacce irin hira. Ki ke tantance labari kafin ki ba shi. Ki kasance mai kama kanki a gabansa.
Kar da ki yarda ya san wani sirrinki wanda mijinki ne na aure kawai ya kamata ya san shi, ko da kuwa a na saura awa guda a ɗaura muku aure ne, balle a haɗuwarku ta farko ko a rayuwarku ta soyayyar samartaka da 'yammatanci.
Wannan 'yar shawara ce, kar da ku ɗauka iyakacinta kenan. Ku yi hankali da dafin soyayya, domin kuwa ya fi dafin maciji illa.
Ina yi muku fatan alheri.