Friday, 9 August 2024

Kyawawan Kalaman Hikima Ga Daliban Ilimi

Tura Wannan Zuwa Ga

Daure ka zama tamkar mai sayar da turaren nan da aka ce mai ƙamshi, ta hanyar amfanar abokin karatunka da maganganun ilimi a duk lokacin da kuka haɗu. 


Kalaman hikima ga ɗalibai
Hoto: Retail

MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Kar da ka kasance tamkar wannan maƙerin, ta hanyar cutar da abokin karatunka da maganganu marasa amfani da amfanarwa a lokacin da ake tsaka da karatu ko bayan haka.


Yi abota da kowa a cikin makaranta amma kar da ka yi saken da har halayensu marasa kyau za su yi tasiri a kanka, hakan zai ba ka damar sanin halayen mutane daban-daban, tare da sanin dabarun zama da jama'a.


Kar da ka kasance ƙarƙashin kulawar wani a kullum, wato ya kasance komai shi yake saya maka a cikin makaranta hakan zai jawo zubewar kimarka a idonsa da sauran waɗanda suka san haka. Kuma za ka kasance a ƙarƙashin sarrafawarsa. 


Amma dai masu iya magana sun ce "Zaman duniya tamkar rumbu ne, miƙo mini na miƙo maka."


Ya kasance a kullum abokinka shi ne wanda yake zaburar da kai a kan karatunka, domin kuwa wannan shi ne masoyinka mai son ci-gabanka, kodan masu iya magana sun ce "Abokin damo guza".


Duniya ba ta auren rago.


Ba a bori da sanyin jiki.


Lokacin abu a yi shi.


Mai tsoro ba ya suna.


A saboda haka ka sance jajirtacce a kan abin da ka sanya a gaba komai wahalarsa, watarana sai labari.


Akwai wasu masu ɓata ruwa ba dan su sha ba. Kasance cikin shirin bijirewa ra'ayi irin na baƙin bajimi mai ɓata garke. 


ALLAH YA BA MU SA'A.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user