Kasancewar bai taɓa haihuwa ba, Sarki ya sa aka tara masa yaran ƙauyen duka domin ya zaɓi ɗaya da zai riƙa idan ya girma ya gaje shi. Da ya yi musu jarabawa, sai yara goma suka yi nasara. Ya ce wa yaran nan, "zan yi muku jarabawar ƙarshe wanda duk Allah ya sa ya ci, shi ne sarki bayan raina."
Marubuci: Bukar Mada
Aka kawo ƙwayoyin masara, Sarki ya ba kowane yaro ƙwaya ɗaya, ya ce su shuka a cikin ƙoƙo bayan sati biyu su kawo ya ga wanda ya fi kulawa da nasa. Yara duk suka ruga gida suka shuka masara, suka yi ta tarairayar ɗan tsiron da ya fito.
Audu ya yi baƙin ciki ƙwarai da tasa shukar ba ta fito ba. Sauran yara suka ba shi shawara, ya samu wata ƙwayar masarar ya shuka. Iyayensa suka hana shi, suka ce, "kul! kai dai tsare gaskiyarka."
Bayan mako biyu yara suka taru a fada. Sarki ya fito yana duba tsiron kowa. Kowane yaro ya tambaya, "wannan ita ce ƙwayar da na ba ka?" Sai yaro ya gyaɗa kai. Da ya zo gun Audu, sai ya ga ƙoƙonsa babu komai. Ya tambaye shi me ya faru da tasa ƙwayar?
Audu ya sunkuyar da kai ya ce, "na shuka kamar yadda ka ce ya Sarki, ga shi tsawon mako biyu ba ta fito ba."
Sarki ya kama hannun Audu, ya ja shi har gaban karagarsa, ya ce wa mutane, "Ku sani cewa ƙwayoyin masarar da na ba yaran nan dafaffiya ce, babu kuwa yadda za a yi dafaffiyar ƙwaya ta tsiro. Wannan yaro shi kaɗai ne wanda ya tsare gaskiya da amanar da na ba su. Don haka shi ne magajina ko bayan raina. Ba abin da aka fi so ga shugaba irin tsare gaskiya da riƙon amana."