Thursday, 22 August 2024

Manyan Shubuhohi 8 Na Zamani

Tura Wannan Zuwa Ga

A wannan zamani namu babu shubuhohin da suka fi yaɗuwa da karɓuwa a wajen mabiyan Shaiɗan kamar Shubuhohin kore samuwar Allah Ta'ala da ƙaryata dukkannin addinai da kafirce musu , da kuma ƙaryata sahihan hadisan Manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da yin fatali da fannonin iliman Tafsiri da Hadisi da Fiƙhu wajen fahimtar addini. 


Shubuhohi 8 Na Zamani
Hoto: iStock


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Shaiɗan da mabiyansa ba su taɓa yin ƙasa a gwiwa ba wajen ƙago shubuhohi da yaɗa su a cikin al'umma.


Manyan Shubuhohin masu ƙaryta hadisai sahihai na wannan zamani namu su ne: 


1. Da'awar cewa Ƙur'ani kaɗai ya isa a yi musulunci da shi ba sai an haɗa da hadisi ba. 


2. Da'awar cewa wasu hadisan sun saɓawa Ƙur'ani mai girma. 


3. Da'awar cewa wasu hadisan wai sun saɓawa hankali. 


4. Da'awar cewa wai hadisan sun saɓawa ilimin kimiyya. 


5. Da'awar cewa hadisan sun saɓawa tarihi ko kuma abin da yake faruwa a yanzu (واقع) wato lokacin su ya wuce sun yi esfaya (expire)


6. Zargin Sahabbai da Tabi'ai da Malaman hadisi da na Fiƙhu da ƙirƙirar hadisai da hukunce-hukunce don daɗaɗawa Sarakuna da ƙarfafa mulkin su. 


A kan haka har ma kafirta Sahabban suke yi ko ce musu fasiƙai ko munafuƙai ko maƙiya Manzon Allah da iyalansa masu yi masa zagon ƙasa. 


7. Munana zato da shakku akan magabata da tabbatattun nassosi. 


Abu na farko da yake zuwa ran su da sun ji abin da bai kama ƙwaƙwalwar su ba, ko ya saɓawa ra'ayinsu shi ne mummunan zato da shakka da zargi da tuhuma, maimakon binciken inganci ko ma'ana ko manufa ko hikima ko bayani daga masana. 


8. Ba su da wasu magabata managarta ko malamai sai su kan su da kuma tsirarun fanɗararrun mutane da kuma kafirai da suka ƙago shubuhohin suke yaɗa su irin su Mahmud Abu Rayyah , Mabiya addinin Shi'a Goldziher, Morgolioth da sauran su. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user