Don Talatu ba ta da saurayi, ba zai sa kawai ta fara son kowanne Audi ba. Abin da nake nufi shi ne ka yi nasarar gano gurbin abin da babu a kasuwa, to amma ko akwai mai buƙatar sa idan ka kawo shi?
Marubuci: Bello Galadanchi
Kasuwanni da yawa a cike suke. Kusan kowace sana’a akwai mutane da yawa da ke yin ta, kuma duka kwastoma ɗaya suke bi.
Saboda haka akwai gasa, kuma wannan gasa tana rage adadin ribar da ake samu.
Sai kawai ka gano wani sabon gurbin abin da babu a kasuwa, wanda ya sa ka fara hangen riba mai yawa.
To amma shin wannan gurbi na da masu buƙata isassu da zai sa har ka iya samun riba?
Akwai gurbi a cikin kasuwa, amma shin akwai kasuwa a cikin wannan gurbi?
Talatu budurwa ce, ba ta da saurayi, amma ba za ta fara son kowane Audi ba.
A dabarar kasuwanci, babu abin da ya kai samun gurbi a sana’a ko kasuwa wanda babu wanda yake gasa da kai. Sai dai abun takaici, wannan gurbi da na saka wa suna “gurbin kasuwanci” na da matuƙar wahalar ganowa, kuma samun alheri daga irin wannan gurbi ya zama kamar mafarkin asuba wanda ba ya taɓa zama gaskiya.
Duk da cewa gasa a cikin rayuwar mu take, a gaskiya tana sa kasuwanci da sana’a na ƙara wahala, yanayin da kullum yake sa mutum yake rage farashi, da hauhawar kuɗaɗen kashewa domin neman sababbin kaya ko gudanar da talla, da kuma tunanin yau da kullum na yadda mutum zai yi fice kuma ya tsere wa waɗanda yake gasa da su.
A wani ɓangaren kuma, kowa ya san irin alherin da ke cikin samun gurbi a kasuwa, ɗan ƙaramin gurbi wanda ba ka da kowa wanda yake gasa da kai; sai irin farashin da ka ga damar sakawa da kuma riba mai yawa irin yadda ranka yake so.
Gano gurbin kasuwanci da kuma kasancewa mai zuciya da juriyar ɗan kasuwa su ne abubuwa biyu da suka fi muhimmanci domin a samu nasara idan za a fara kasuwanci. A shekara ta 2006, wanda ya samar da dandalin Twitter (X) mai suna Jack Dorsey ya gano gurbin kasuwanci inda ya haɗa sohiyal media da taƙaitaccen saƙo domin samar da sabon tsari irin wanda babu wanda ya gano a duniya. Kyauta ne amfani da dandalin ga duk wanda yake so ya yi amfani da shi, amma kuɗaɗe na shigowa daga kamfanoni waɗanda suke so a yi musu talla. Kamfanin Twitter ya samu dala miliyan 582 daga talla kawai a shekara ta 2013.
Ba kowanne gurbin kasuwanci ba ne yake da alheri. Akwai wani kamfani da ya ƙirƙiro mota mai iya tafiya a cikin rafi a shekarun 1960. Sabon abu ne a lokacin, amma kwastomomin ba su da yawa kwata-kwata kuma hakan ya sa ko ribar Nera ɗaya kamfanin bai samu ba. Haka zalika wani kamfani a Amurka da ya ƙirƙiro ruwan sha na dabbobi bai bai wa kowa sha’awa ba.
Don kawai ka gano wata sana’a ko gurbin kasuwancin da babu wanda yake yin shi, kar ka yi tsalle ka jefa kanka a ciki. Amma kuma, kullum, ka yi yunƙuri da binciken wani sabon gurbin kasuwanci wanda babu shi, kuma jama’a suna buƙata. Wannan shi ne zai sa ka zama biloniya.