Monday 5 August 2024

Sirrin Yadda Ake Rubuta Wasikun Soyayya Masu Ratsa Zukatan Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

Shin ko ka taɓa samun saƙon wasiƙar da ka karanta kuma kake maimata karantawa kullum, har ba ka iya ɗauke ganin ka saboda jin daɗi?


Rubuta wasiƙar soyayya
Hoto: Cafemom


MarubuciImran Musa Jahun

Shin ka taɓa karanta wasiƙar da ta juyar da  tunanin ka ta saka zubar hawaye?


Idan ka taɓa samun irin wannan wasiƙar to lallai ka san ƙarfin da ke cikin rantsattsiyar wasiƙa.


Rubuta wasiƙar soyayya a wannan zamani ya zama ruwan dare musamman shigowar wayar salula.


Sai dai da yawa kan kasa rubuta wasiƙa 

ingantacciya ga masoyi. 


A wannan shafin zan koya maka yadda ake tsara wasiƙar ban girma.


Zan kawo maka hanyoyi daki-daki, su za ka bi ka zama ƙwararren marubucin wasiƙar soyayya. 


TUNANIN KU


Zahiri masoyin ka shi ne a kullum abin tunanin ka, shi ne ko ita ce dalilin da ya sa

kake jin za ka rubuta wasiƙa.


Wasu mutane suna kunna waƙoƙin soyayya ko wata waƙa da suke ganin tana da tasiri da soyayyar su kafin su rubuta wasiƙa. 


Kallon hoton sahiba yana taimakawa ƙwarai a yayin da kake rubuta mata wasiƙa.


Ka tsaya ka nutsu ka san abin da sahibar ka ke so, shin mene ne ya fuzgi zuciyarka da har ka ba ta masauki a cikin ta? Mene ne yake burge ka game da sahibar taka?


Dukkanin waɗannan tambayoyi za ka amsa su a cikin wasiƙar ka. 


Ga misalin irin ta nan kamar haka:


Zuwa ga kamilallar mace mai kyau da tsarin siffa, Amina.


Bayan gaisuwa mai ɗauke da shauƙin jin

yadda kike da yanayin da fuskarki take, ina miki fatan alkhairi a cikin wannan wata mai albarka. 


A kowanne lokaci na zauna ba ni da wani tunani idan ba naki ba, na kan tuna irin murmushinki da dariyar da kike mini.


Na kan tuna irin kallon da dara-daran idanuwanki ke min da ke fizgar imanin zuciyata, haƙiƙa na yi dace da samun kyakkyawar mace abar kwatance. 


Zan kasance tare da ke a duk inda kike, cikin mafarkinki, cikin tunaninki, cikin farin ciki da baƙin ciki.


Zan kasance mai share miki hawayenki, ta ya ya ma za ai na bar idanuwanki su zubar da hawaye? Komai na jikin ki yana da muhimmanci a gare ni. 


Fatana ki kasance cikin farin ciki da annashuwa, fatana ki zamto tauraruwar da ke haske duniyar mutane.


Ke ce tawa har abada, ki huta lafiya.


Idan ku kai duba da wannan wasiƙar, an gina ta ne da irin tunanin da marubucin yake a kan sahibar shi, ya gaya mata dalilin da ya sa take ƙara shiga zuciyar shi. 


To, duka duka anan zan tsaya, sai mun sake

haɗuwa a tsarin rubuta wasiƙar soyayya kashi na biyu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user