Marubuci: Dr. Mansur Sokoto
Ya kai ɗana! Ka sani cewa, watarana tsufa zai kama ni. Zan riƙa yin abubuwa ba yadda aka saba ba. Ka sa haƙuri sosai don ka fahimce ni.
Ya kai ɗana! Idan ƙafafuna suka kasa ɗauka ta, ka tuna lokacin da na riƙa ɗaukar ka har hannayena su yi sanyi. Idan na so ka sauka sai ka ce ba ka sauka. Na kan yi ta rarrashinka a wancan lokaci don in samu yardarka. Kada ka ji kunyar riƙe hannuna ko rungumata a wannan lokaci. Watarana kai ma za ka buƙaci mai yi ma ka haka.
Ya kai ɗana! Idan wancan lokacin ya zo hannuna zai kasa riƙe abinci, sai yana zuba a kan tufafina. Zan kasa cire ma kaina tufafi bayan na lalata su ballantana in iya sanya wasu. Ka yi haƙuri da ni. Ka tuna lokacin da na koya maka abinda yanzu na kasa iyawa.
Ya kai ɗana! Idan ka tuna wani laifina a gare ka, ka iya fahimtar cewa, ban yi shi don in musguna maka, ko in ƙetace ka ba. Na yi ne don na koya maka zaman duniya da yadda za ka zama cikakken mutum. A yau babban abin da za ka yi min shi ne ka manta da kurakuraina, ka yafe laifukana. Ina fatar Allah ya yafe naka kurakurai, ya gafarta laifukkanka.
A wannan lokaci zan kasa yin tsafta yadda kake buƙata. Kada ka manta ni ne na koya maka yin tsafta da kwalliya da shafa turare.
Kada ka yi dariya idan ka ga ina yin wauta, ko na kasa gane abubuwa yadda ya kamata. Ka zama kai ne ƙwaƙwalwata da idona da kunnuwana don in gane abubuwa.
Ka tuna cewa, ni na koya maka zaman duniya da yadda ake jin daɗin rayuwa. Don me ba za ka yi haƙuri idan na buƙaci wannan koyarwar ka koya min ba?
Ya kai ɗana! Idan na tsufa zan daina fahimtar al'amuran duniya yadda ya kamata. Zan riƙa jiran mutuwa ne a kowane lokaci. Kada ka gajiya wajen taimakona domin wata babbar ƙofar aljanna ce Allah ya buɗe maka.
Idan lokacin da nake faɗi ya zo tunanina zai yi rauni, ƙasusuwan jikina za su yi sanyi, harshena zai yi nauyi. A lokacin kuma babu abinda nake so sai kusancinka da jin ɗuriyarka. Yi ƙoƙari ka taimaka min don biyan buƙatata. Ko a wannan lokacin na san abinda nake so a raina kodayake ba lalle ne in iya faɗa maka ba.
DUBA WANNAN: Karanta Wasiyyar Wani Uba Mai Hikima Ga Dan Sa a Zamanin Internet
Daga ƙarshe, ina sanar da kai cewa, da dai ba ni da farin cikin da ya fi jin daɗinka, da ganin farin cikinka da murmushinka. Kada ka bari idan zan bar duniya na bar ta da baƙin cikinka ko ɓacin rai a kanka.
Allah ya yi maka albarka, ya sa ka gama da ni lafiya, ka samu wadatar arziki da jin daɗin rayuwa.