Monday 30 September 2024

Abin Da Ya Kamata Sabon Dan Kasuwa Ya Sani

Tura Wannan Zuwa Ga

Akwai dalilai da yawa na fara kasuwanci. Akwai mutane da yawa waɗanda ba sa son yi wa gwamnati ko kamfani aiki, sun gwammace su samu kuɗi daga abin da ransu yake so, ko nuna irin basira da fasahar su, ko kuma yin arziki da gumin su. Duk da cewa “idan har kana da ƙaton burin yin abu, to za ka iya”, dole na bayyana cewa ƙoƙarin cimma wannan buri yana da haɗari.


Idan har kana da ƙaton burin yin abu. To za ka iya, ƙetare siraɗi a fara sana'a.
Hoto: Ast consulting

MarubuciBello Galadanchi


Dole duk wanda zai ɗauki wannan aniya, sai yana da zuciyar ɗan kasuwa, da ƙarfin hali na ajiye aikin da yake samun albashi, ya fita shi kaɗai, ya tunkari rayuwa mara tabbas. Wasu mutanen kuma na buƙatar a tunzura su, kamar idan aka kori mutum daga aiki, sai a ga ya yi zuciya ya fara sana’a.


A halin yanzu ba kamar lokutan baya ba, matasa da yawa sun rungumi kama sana’a hannu biyu-biyu. Wasu daga cikin su sun laƙanci ilimi da dabarun kasuwanci tun suna da shekaru goma sha wani abu, kuma suna jin daɗin hakan da ‘yancin tafiyar da sana’ar su. 


Sai an yi imani
Hoto: Bates group

Duk da cewa akwai dalilai da yawa na fara kasuwanci, abin da duk wani ɗan kasuwa yake da shi shi ne zuciyar yin kasada. 


Mutane kaɗan ne suke samun nasara a karon farko, kuma dole sai an jajirce koda ana ji ana gani, kasuwancin ba ya tafiya yadda ake so, kuma sai an ci-gaba da bada himma da yin murmushi da kalamai masu daɗi, da haƙuri a gaban kwastomomi da waɗanda suka ba ka jari a duk lokacin da suka ce “a’a”. Yin imani dangane da sana’a na da matuƙar muhimmanci ga nasara. Babu shakka akwai sana’a’o’i da yawa da ba su buƙatar jari mai yawa, amma kusan dukansu na buƙatar ‘yan kuɗi a farko.


Dole sai sabon ɗan kasuwa ya tabbatar wa iyaye da ‘yan uwa, ko abokai, ko banki, ko Oga, ko kuma duk wani wanda shi ne zai bada jari cewa wannan sana’a sahihiya ce, wato za ta haifar da alheri mai yawa, duk da cewa hakan zai iya ɗaukar lokaci.


Ko kun san cewa sai da kamfanin Amazon ya yi shekaru shida kafin ya fara samun riba?

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user