Sanin waɗannan abubuwa ashirin ɗin za su taimake ku a rayuwa.
1. Kada ka je inda ba a gayyace ka ba. Kuma idan an gayyace ka, kada ka wuce gona da iri.
Marubuci:- Idris Abubakar Idrisia
2. Ka daina maula a wajen mutane.
3. Ka daina surutu fiye da yaddda ya kamata.
4. Idan mutum ya wulaƙanta ka, koda a rashin sani ne, ka sanar da shi kaitsaye.
5. Kada ka ci abincin mutane fiye da yadda suke cin naka.
6. Ka rage yadda kake ziyartar wasu. Musamman idan su ba sa ziyartar ka.
7. Ka zuba jari, koda kuwa ba yawa. Ka farantawa kanka rai ba sai ka dogara da wani ba.
8. Ka daina yin maganar wasu mutanen, idan ba sa wajen.
9. Ka yi tunani kafin ka yi magana. Kashi 80% na yadda mutane ke daraja ka shi ne ta abin da ke yawan fitowa daga bakin ka.
10. Koyaushe ka zama mafi kyawu. Ma'ana cikin tsafta. Ka kasance cikin ado da kwalliya yadda ya kamata.
11. Ka kasance mai yawan kyauta. Ka shagaltu da cimma burin ka.
12. Ka girmama lokacinka.
13. Kada ka zauna a cikin mutane da dangi wanda ba su ɗaukar ka da kima. Ka tafi ka bar su.
14. Ka koyi kashe kuɗi a kan kanka. Ta haka ne mutane za su amfane ka kuma su ba ka girma.
15. Ka kasance mai rauni wani lokacin.
16. Ka kasance mai bayarwa fiye da mai karɓa.
17. Ka daina neman wanda ba ya nemanka.
18. Kake yi wa mutane daidai da abin da suka cancanta.
19. Indai mutum ba ya bin ka bashi to zai kira ka a ƙalla su byu. Idan har da gaske yana ganin darajar ka.
20. Ka kyautata ga duk abin da ka kasance kana aikatawa. Kasance mafi kyau.
Allah ka tsare mana mutuncin mu da girman mu, ka wadata mu da arziƙi mara yankewa duniya da lahira.