Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah ɗan ƙabilar Banu Amar. Qays ya kasance mai fasaha da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad an fi kiran ta da Laila Amiriya, a hankali ya riƙa nuna mata soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu.
Marubuci:- Auwal Ilyas Adam
Duk lokacin da ta makara zuwa makaranta sai hankalinsa ya tashi ya rasa sukuni, gabaɗaya sai ya zuba wa ƙofa ido ba ya mayar da hankali ga karatunsa. Wata rana da zuciyarsa ta cika da bege, ya ji ƙirjinsa kamar ya fashe, bai san lokacin da ya riƙa rubuta sunan Laila a takardar rubutunsa ba maimakon abin da ake koya musu. Ɗalibai da suka ga haka sai suka haƙiƙance lallai ya yi nisa wajen ƙaunar ta. Da haka ita ma Laila ta soma ƙaunarsa ya zamana duk makarantar an san su a matsayin masoya.
Shi Qays kamar tun yana yaro ƙarami masu ilimin taurari suka bayyanawa mahaifinsa cewa zai kasance wanda rayuwarsa za ta faɗa cikin wahala da musiba. Suka ƙara da cewa idan ba a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa. Tun daga wannan lokacin mahaifinsa ke samo masa laƙani da magunguna da addu’o'i. Yayin da ya data sai mahaifinsa ya ɗauke shi ya kai shi Dimashka karatu inda anan ne ya haɗu da Laila.
Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban ƙabilar Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa ga maciji da ƙabilar su Qays. Laila da Qays suka zama tamkar jini ɗaya tsoka ɗaya, idan ɗaya bai ga ɗaya ba sai ya kama rashin lafiya, amma Qays abin na sa ya fi tsanani, domin kuwa har waƙoƙi yake rubutawa masoyiyarsa yana karanta su a ko’ina.
Ɗaya daga waƙoƙin da ya yi mata ita ce:
Na so ki ya mai kyau dan gaske.
Wane wata ko tauraro mai haske.
Kin shiga ruhina kin mammallake.
Idan babu ke to ni kuwa na hakkake.
Ba za ni rayu a duniyar nan ba.
A makaranta aka rinƙa gulmar su ana nuna Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan ka yi masa abu ka ce masa ya yi haƙuri don Laila, shikenan zancen ya wuce. Da ɗalibai suka gano lagonsa, suka riƙa ɗauke masa kayan rubutu suna cewa ya ba su domin darajar Laila. Ba musu sai ya ba su. Maubin (malamin) makarantar ya damu ƙwarai da irin wannan al’amari. Musamman da ya ga Qays wanda yanzu sunan ya ɓace ya koma Majnun Laila (Mahaukacin Laila) ya rubutawa iyayensu takarda yana faɗakar da su halin da ‘ya’yansu ke ciki. Iyayen Laila suka cire ta daga makarantar aka kirawo wani ƙwararren malami yana koya mata karatu a gida. Ciwon so ba shi da magani! Maimakon hakan ya yi magani sai ya daɗa rikita al’amari. Majnun ya daina karanta komai kullum sai kuka sai waƙa, duk abin da ya gani sai ya ga yana masa gizo da kamannin Laila. Nan da nan sai ya soma rera waƙar so gare ta.
Mahaifin Majnun ya zo takanas ya ɗauke shi zuwa wajen likitoci da ‘yan tsibbu da bokaye da sauran masu da’awar magani duk abin ya zama tamkar wutar kara ana yayyafa mata fetur.
Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin Laila amma duk a banza. Wani daga baffaninsa ya ce masa, “Wai kai Qays me ka gani a jikin Laila da ka nace mata haka? Ka zo mu je na nuna maka mata dubu waɗanda suka fit a kyau da kyan fasali da asali da mulki da dukiya da sarauta ka zaɓi wadda ta yi maka.” Majnun ya dube shi ya girgiza kai ya ce, “idanun Majnun Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.” Ya ɗaga hannu sama ya ce, “Ya Allah! Na san ba ka yi kyakkyawa a duniyar nan tamkar Laila ba. Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da suka zo duniya shan iska. Ya Allah alƙawarinka ba ya tashi, na tabbata daga kan Laila ba za ka sake wata kyakkyawa ba. Ya Allah ka ba ni Laila!”
Wani daga ƙabilarsu ya ba mahaifin Majnun shawarar ya ɗauki Majnun zuwa Makka ya yi roƙo a ka’aba kan Allah ya ɗauke masa son Laila a zuciyarsa. Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je ɗakin ka’aba sai mahaifinsa ya ce masa: kama tufafin ka’aba ka roƙi Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama ya ce: “Allah na tuba gare ka daga dukkan laifi, amma ba zan tuba daga son da nake yi wa Laila ba . . . Ya ƙara da cewa, “Ko Luqman, babban malami masani na tabbata ba shi da maganin ciwon so…Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke tsakanina da Laila. Ya rera waɗannan baitoci:
A Makka na ce da shehin malami, Wai shin wace ke cutar da ni?
Shin laifi ta ke yi to a sanar da ni.
Shehi ya ce “ɗana bi a hankali, Azaba na nan zuwa can gare ta.".
Na yi farat na ce masa “A'a na yafe, Da azaba ta samu Laila ko a gefe, ba ni ƙauna, gara ta same ni a gefe. Da na daina sonta a barci ko farke, gara na mutu da ciwon ƙaunar ta. Sannan ya ce da murya mai raurawa, “Allah ka ba ni Laila!”
Yayin da iyayen Majnun suka ga haka kullum lamarin nasa ƙara lalacewa ya ke yi, sai suka ga babu mafita face su je su nemi auren Laila wurin iyayenta. Wannan shi ne mataki na ƙarshe da suke ganin zai magance matsalar ɗansu.
Suka tashi jakadu na musamman zuwa garin su Laila suka bayyana musu irin halin da ɗansu yake ciki game da soyayyar Laila. Sannan jakadun suka nemi aurenta dominsa. Iyayen Laila suka amsa da cewa, “mu a wajenmu abin da Majnun yake yi domin ‘yar mu wulaƙanci ne mai girma. Kuma duk da yake mun san cewa Laila tana da ra’ayinsa amma ba za mu iya aurar da ita gare shi ba. A dalilinsa mun cire ta daga makaranta, mu a wajenmu, mahaukaci ne kaɗai zai riƙa irin abin da Majnun ke yi.”
Da haka iyayen Majnun suka ji daɗi tunda su a tsammaninsu idan har ya daina shiririta za su amince su aura masa ita. Saboda haka suka shiga tausasarsa suna ba shi shawarar ya nutsu ya daina abubuwan da yake. Majnun ya amince da haka, amma da sharaɗin za a kai shi ya ga abar ƙaunarsa Laila.
Suka shirya suka tafi tare da wakilansa zuwa garin su Laila. Aka sauke su a wani babban gida sannan aka kawo musu abinci da abin sha. An ƙawata wajen da fitilu masu launi iri daban-daban. Sannan a kunna turaren wuta ko'ina sai ƙamshi ke tashi. An jera kasake masu yawa cike da abinci da fulawoyi masu ƙayatarwa. Zuciyar Majnun kuwa ta kasa nutsuwa, ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya tafi ga masoyiyarsa.
Bai iya jurewa ba sai ya miƙe a gaban waliyan Laila ya riƙa safa da marwa yana rera waɗannan baitoci:
Na yi nisan zango don na gane ki.
Ga shi na zo nan ina ta biɗar ki.
Ina kike ina kika shiga ne in gan ki.
Zuciyata tana ta jidali domin nemanki.
Ya ki taho abar begena don Allah nunan kanki.
Jimawa kaɗan sai ga karen da Laila ke zuwa da shi makaranta ya shigo gidan. Majnun sai ya ji ya kasa jurewa, ya zabura wajen karen nan ya rungume shi yana sumbatarsa yana cewa, "Na ga rabin Laila saura rabin. Ya karen nan mai baiwa maza je ka ingizo min Laila."
Garin wutsulniyar da kare yake yi da ƙafafu ya ture farantan abincin, suka ɓata gaban rigar wani dattijo mai faɗa aji a dangin Laila. Shi kuwa gogan naka sai ya ɗauki wani tsiron fulawa ya maƙalawa karen a wuya yana ce masa, "Maza je ka kai wa Laila ka miƙa min gaisuwata gare ta." Duk jama'ar wurin suka yi tsit suna kallon ikon Allah.
Wakilan da suka rako shi suka rasa inda za su sa kansu domin kunya.
Wakilan Laila kuwa suka cika da fushi iyakar fushi. Wani daga cikinsu ya fusata ya ce wa Majnun, "Shin bautar kare ka zo ko kuwa maganar aure?"
Kaitsaye Majnun ya kalli mutumin ya ce, "Wannan karen a wurina ya fi mutum dubu daraja, domin a jikinsa ina ganin surar masoyiyata wadda ƙaunarta ke ɗamfare a zuciyata dare da rana." Duk wuri aka ɗauki salati. Jama'a suka riƙa zunɗensa suna cewa ya haukace. Dattijon nan da aka ɓatawa riga da abinci ya miƙe a fusace ya fice daga gidan. Duk jama'a ma suka watse.
Da wannan jama'a suka riƙa rantsewa cewa haukan nan dai bai rabu da shi ba, sai ma abin da ya yi gaba. Daga nan iyayen Laila suka fito kaitsaye suka ce ba za su aurar da 'yar su ga Majnun ba.
To daga nan sai duk wani fatan samun nutsuwarsa ya zama sharon gayya, suka haƙiƙance ba za su iya magance masa matsalar ba, don haka suka sa masa albarka suka ƙyale shi bisa halinsa. Shi kuwa duk inda ya shiga lungu da saƙo sai ya riƙa cigiyar Laila ko sun san inda take da yadda zai sadu da ita. A haka har ya yi kiciɓis da wani Jakada mai aikin raba takardu. Ya tambaye shi labarin Laila. Jakada ya ce masa "Laila da iyayenta sun tashi daga garinsu sun koma wani gari mai nisa, daga nan garin zuwa can tafiyar mil dari da ashirin ne." Majnun ya shiga yi masa magiyar yana ba shi saƙo zuwa gare ta.
Jakada ya amince zai karɓi saƙon takarda kurum babu wani abu. Majnun ya zauna ya yi ta rubutun shafuka da yawa, har Jakada ya gaji ya ce masa, "Wacce irin wasiƙa ce haka?"
Majnun ya ce, "Wasiƙar soyayya ce ba ta da ƙarshe."
Jakada ya yi dariya da haka sannan ya ce, "To samu waje ka ɗiga aya ka ba ni na tafi." Majnun ya naɗe takardar ya ba shi. Sannan ya nemi ya yi masa rakiya kaɗan. Suna tafe Majnun na ba wa Jakada labarin abar ƙaunarsa Laila shi kuma yana ta mamaki. Sai da suka shafe mil goma Majnun na tafiya a ƙasa Jakada na bisa raƙumi.
Jakada ya ce masa, "To ka koma haka, ka yi nisa ƙwarai da gidanku." Majnun ya juyo ya soma tafiya sannan ya juya ya ce da Jakada da babbar murya, "Ya kai ƙaunataccen abokina! Wallahi na yi mantuwar wani muhimmin saƙo da nake so na rubuta mata!"
DUBA NA GABA ANAN: Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (2)
Jakada ya ce, "To gaskiya ba zan tsaya ba, sai dai ka faɗa min da baki na faɗa mata".
Za mu ci-gaba Insha Allah.