Mene ne yake hana jama'a samun nasarori a kasuwanci?
Babu shakka wannan tambaya ce da ake ƙoƙarin amsawa tun iyaye da kakanni.
Misali yanzu kana Kano kuma kana so ka je Legas, sai aka ce maka ai Ikko tana kudu maso yammaci da Kano. Ka ga kuwa idan ka kalli wannan alƙibla ka miƙe, wannan zai kasance hanya mafi sauri da sauƙi domin isa Legas. Duk wanda ka tambaya a Kano, zai ce maka Ikko tana kudu maso yammacin Najeriya.
Marubuci: Bello Galadanchi
To amma fa akwai abu ɗaya. Ba ka taɓa zuwa Legas ba, kuma ba ka san hanya ba.
Saboda haka dolen dole sai ka gano hanya da kanka.
Yanzu mene ne abin yi?
Abu mai sauƙi, ai kawai ka kalli kudu maso yammacin Najeriya ka fara tafiya da fatan hanyar a miƙe take daga Kano zuwa Legas babu kwana ko tsayawa, sai dai kuma ashe abun ba haka yake ba. Wani lokacin hanyar a miƙe take, wani lokacin kuma sai ka iso kwanar Jebba ka rasa hanyar da za ka bi. Duk wanda ka tambaya zai ba ka irin nashi kwatancen.
Shin miƙe wa za ka yi ko kuma kwanar hagu za ka ɗauka, ko kuma kwanar dama? Nan take ka lura cewa hanyar a cinkushe take, kuma ba kai kaɗai ba ne kake son zuwa Legas, kowa ma so yake ya je kuma tsere ake yi. To fa!
Wasu matafiyan ƙoƙarin ture ka suke yi daga kan hanya, wasu kuwa ƙoƙarin "overtaking" ɗinka suke. Wasu ba su damu ba ko za ka faɗi ka mutu.
Yanzu tambayar anan ita ce maganar wa za ka amince da ita?
A kan hanyar ka ta zuwa Legas, za ka haɗu da mutane iri-iri masu yawa. Za ka haɗu da direban Ƙatuwar Mota wanda ya ce maka ya san wata gajeriyar hanya. To dama a rikice kake, saboda haka sai ka yanke shawarar bin direban domin tafiya Legas ta 'yar karamar hanya.
Cikin ɗan ƙaramin lokaci sai ka fara farin cikin bin wannan direba, saboda hanyar babu kowa a kanta kuma komai na tafiya yadda ya kamata. Can kuwa sai kuka ci karo da sanarwa da ke cewa BABU HANYA. Ashe gajeriyar hanyar da kuke nema duk labarin gizo da ƙoƙi ne.
Yanzu me za ka yi?
Duk baƙin ciki da takaici ya kama ka, ranka ya ɓaci. Duka za ka yi wa direban mota ko kuma zagin shi za ka yi? Koma me za ka yi, kuna waje ɗaya ne cak! Babu motsi!!
Wasu daga cikin ku za su juya su koma da baya tunda Legas kuke son zuwa, kuma babu abin da zai dakatar da ku. A kan hanya kuwa za ka ga abubuwa masu ban sha'awa da ban mamaki, wani lokacin kuma za ka ga abubuwan al'ajabi da tausayi kamar hatsarin mota. Za ka ga mutane suna mutuwa, wasu na bara, wasu na dariya, wasu na tsokana. A taƙaice za ka ga jama'a a cikin yanayi iri-iri kamar soyayya, ƙiyayya, son zuciya, jimami, ƙarfin gwiwa da sauransu.
Amma jira, ai Legas kake so ka je ko? Saboda haka dole sai ka yi bankwana da waɗannan mutane ka mayar da hankalin ka akan abun da ya fito da kai. Legas!!!
Idan ba ka ci-gaba da tafiya ba, ba za ka samu damar zuwa Ibadan ba, sai dai ibadan ta burge ka, kuma ka ji labarin cewa Legas a cunkushe take da jama'a. To ko za ka haƙura ka zauna a Ibadan ne? Wasu daga cikinku za su zauna a Ibadan ba tare da ƙarasawa Legas ba.
Kai ma ka yanke shawarar zama, amma kusan kullum sai ka yi tunanin abin da ya fito da kai. Wannan kuwa ya hana ka sukuni, shi ne wata rana ka haɗa kayanka ka hau hanya. Jama'a sun ce maka Legas ba ta da nisa daga Ibadan. Hanyar fayau babu kowa, amma kafin ka ci rabin hanya, komai ya cinkushe. Manyan motoci da ƙanana. Nan take ka fara nadama. Me yasa ka bar Ibadan? Ba ka da godiyar Allah ne? Da hanyar tana da kyau, da kusan duka mutanen Ibadan sun koma Legas. Ba ka tsoron 'yan fashi ne ko hatsari?
Idan har ka cire duka waɗannan ƙalubale, to ba za a wayi gari ba za ka samu kanka a cikin Legas.
To idan muka komo tambayar mu ta farko, ko mene ne yake hana mutane da yawa samun nasarori a kasuwanci?
1. Wasu sun tsaya ne saboda sun fi sha'awar Ibadan.
2. Wasu kuwa sun tsaya ne saboda suna ƙyashin kashe kuɗin su, ko kuma tsoron haɗarin mota.
3. Wasu kuwa motar su ce ta lalace.
4. Wasu sun ɗauki hanyar wani gari daban a kwanar Jebba.
5. Wasu kuwa sun bi shawarar direban motar nan ne.
6. Wasu kuwa suna Kano, ko hanyar ba su kamo ba.