Mafi yawancin lokuta, mutanen da ke haɗaka wajen gudanar da kasuwanci na farawa ne ba tare da tsara dokokin da za su zamar musu gimshiƙin gina wannan sana’a tare ba. Komai daɗewa, za su fuskanci cewa rashin tsara dokoki tun farko ya zama dalilin rashin shiri, da takaici, wani lokacin ma har da rigima.
Marubuci: Bello Galadanchi
Abokan sana’a za su iya yin arangama dangane da abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da salon aiki, buri, rarraba aiki da salon shugabanci. Wannan rubutu zai mayar da hankali ne akan yadda ake kafa haɗakar kasuwanci da tafiyar da shi yadda ya kamata.
Tambayar farko da za ka yi wa kanka shi ne, shin kana buƙatar haɗa kai da wani? Mafi yawancin lokuta, za ka haɗa kai ne da wani idan har kana buƙatar shi domin nasarar wannan sana’a – kamar idan yana da kuɗi ko kadarori, ko kuma dangantaka mai kyau ko kuma yana da ƙwarewa a wani fanni na sana’ar da kai ba ka da shi. Idan kuwa babu ko ɗaya, to gwamma ka ɗauki wani aiki a ƙarƙashin ka a matsayin ma’aikaci ko ɗan kwangila mai zaman kansa.
Tun farko, fahimtar juna ta hanyar tattauna komai da komai na da matuƙar muhimmanci a kowanne ɓangare na wannan haɗaka. Babban kuskure da mafi yawancin abokan aiki ke yi shi ne fara sana’a tare kafin su san juna sosai. Dolen dole sai kun fahimci juna, sannan kun iya bayyana ra’ayoyinku da shawarwarinku da tunaninku ga juna hankali kwance.
Idan ba ku taɓa aiki tare ba, to sai ku jarraba junanku ta hanyar gudanar da wani ɗan ƙaramin aiki tare, wanda zai nuna ɓangaren da kuke da ƙwarewa, sannan kuma kuke buƙatar juna domin gabatar da shi. Wannan hanya ce mai kyau na gwada juna domin fahimtar halayya da aƙidu.
An fi so masu haɗaka su kasance sun ƙware a fanoni daban-daban na wannan sana’a, amma kuma suna buƙatar juna, kamar mai wanki da guga. Ga wani misalin; kin iya dafa abinci, amma abokiyar haɗin ki ta iya neman kwastomomi da tallata sana’arku kuma ta san mutane da yawa, abin da ke ba ki iya ba kuma ba ki da shi.
Idan kuna so ku tantance yadda haɗin kai zai kasance tsakanin ku, to ga wasu tambayoyi da za ku iya yi wa junanku, ko abokai ko iyalan juna:
Shin kuna da aƙidu, da shawarwari, da buri iri daya?
Shin kun amince da halayyar abokan haɗakayyar ku?
A wanne ɓangaren rayuwa ta yau da kullum ne kuke da matsaya iri ɗaya?
Za ku yarda ‘ya’yan ku ko abokan zaman ku su ma su shiga wannan sana’a?
Me za ku yi idan ɗaya daga cikin ku ya yi wani abin da bai dace ba?
Me za ku yi idan ɗaya daga cikin ku yana so ya bar garin da zama?
Wani abu mai amfani da za ku iya yi shi ne ku yi balaguro tare, inda za ku tattauna burin ku, domin ganin inda kuke bai ɗaya, da kuma ɓangarorin da kuke da bambanci.
GARGAƊI
Ka yi hankali wajen ƙulla haɗakar kasuwanci da abokanka, ko ‘yan gidanku. Kamar yadda aure ke ƙarewa wani lokacin, haka ma haɗakar kasuwanci na iya tsinkewa da lallacewa cikin tashin hankali. Saboda haka dole ka tantance idan har za ka iya yin kasada da dangantakar ka, domin fuskantar abin da zai biyo baya idan sana’ar ta karye.
Ka fuskanci haɗakar kasuwanci da abokai ko iyalai kamar yadda za ka yi da mutanen da ba ka sani ba. Ka shirya komai daga farko har ƙarshe, sannan ka tsara dokokin sana’a waɗanda ba su da alaƙa da rayuwarku ta yau da kullum.
Idan za ka yi haɗaka ne da matar ka, ko da mijinki, to za ku ga cewa sana’ar tana neman shiga kowanne saƙo da loko na rayuwarku. Sirrin masu nasara a irin wannan haɗaka shi ne, suna da iyaka tsakanin rayuwarsu ta gida da ta sana’a.
Misali shi ne bayan dawowa gida da yamma daga aiki, to za su a je duk wata tattaunawa ta sana’ar har sai yara sun kwanta bacci.
Idan har kuka yanke shawarar fara wannan sana’a, to ku tabbatar kun rubuta yarjejeniya kuma kun rattaɓa hannu. Idan da hali, ku samu lauya ko wani akawu ya taimaka muku. Ku tabbatar kun rubuta wannan yarjejeniya, ko daga ciki ɗaya kuka fito. Mutane da yawa da ke da alaƙa mai ƙarfi na yin watsi da wannan nasiha, saboda a ganinsu, dangantakar da ke tsakaninsu ta fi ƙarfin duk wani ƙalubale da ka iya tunkarar su. Wannan babban kuskure ne. Don Allah ku rubuta yarjejeniya, ku saka hannu akai, kowa ya aje kwafi.
Mafi yawanci, irin wannan yarjejeniya na ɗauke da batutuwan sana’ar mafi muhimmanci. Sun haɗa da albashi, da yadda za a iya fita daga wannan haɗaka, da ayyukan kowa, da kuma kaso nawa kowa ya mallaka.
Shawarar ƙarshe ita ce, ku tabbatar kun kafa dokokin yadda za ku ringa tattaunawa a kowacce rana. Alal misali, za ku iya amincewa akan tattaunawa sau biyu a kowace rana a muhimman lokutan da kuka zaɓa, inda za ku yi bitar aikin da kuke yi da kuma yanke shawarwari. Idan da hali sau ɗaya a watanni biyu zuwa uku, ku yi zama na musamman domin tattauna alƙiblar sana’ar, da yadda za ku ci-gaba da cimma burin ku.
Duk wani abu mai kyau yana da wahala.
Da akwai sauƙi, to da kowa ma zai iya.
Allah Ya bada sa’a.