1. Shirka, ko kafirci ko munafurci babba na ƙin Allah da Manzon sa, da ƙin gaskiya.
2. Bidi'a, ƙaramar bidi'a ko babba, ta aikin zuciya ko gaɓɓai, ko ta lafazi.
Marubuci: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
3. Ragowar manyan saɓo, kamar zina luwaɗi, maɗigo, sata, kisan kai, shan giya, caca, fashi , da sauransu, ya kuma hana mutum yin nadama da tuba.
4. Ƙananan zunubai, domin suna taruwa su zama manya, tunda ana rena su.
5. Shagala da gafala daga abu mai muhimmanci zuwa mara muhimmanci.
Kamar mutum ya shagala da aikin nafila alhalin kuma yana sakaci da farilla.
6. Cusawa mutum tsoro da waswasi , da gudun zargi a kan gaskiya.