Wannan hikaya an ciro tane daga littafin khalila wa Dimna, wani daɗaɗɗen kundin labaru masu faɗakarwa wanda Masani Bipdai ya rubuta tun a zamanin mulkin Annabi Zulƙarnaini.
Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo
Hikayar ta fara da cewa "A wani gari mai suna Baudamana, an yi wani attajiri mai kyauta. Babbar sana'arsa ita ce fatauci, inda yake sayen kayayyaki daga gari zuwa gari.
Sarkin wannan gari na Baudamana inda attajiri yake yana sane da ayyukan karimcin da wannan attajiri ke yi ga jama'a, don haka ma ya janyo shi a jiki tare da naɗa shi matsayin galadima a fadarsa.
Wannan attajiri, ya kasance mai yalwar hannu. Kyautarsa ta game sarakuna da talakawa. Idan ya so, yana iya sanyawa a tara masa talakawa ya yi ta raba musu dukiya, idan kuma ya so, yana iya gayyatar manyan attajirai da sarakuna walima tare da gwangwajesu da kyaututtuka.
Rannan bikin 'yarsa ya taso, sai attajiri ya gayyaci sarkin garin da wasu manyan mutane walima a gidansa kamar yadda ya saba. Wuri ya yi wuri, manyan baƙi duk sun zazzauna akan kujerun alfarma da aka tanadar musu. Sai kwatsam attajiri ya hango wani bawan sarki a kan wata kujera wadda aka tanadarwa manyan mutane, ya harɗe yana shan ƙamshi abinsa. Wannan abu sai ya baƙanta masa zuciya. Tun daga nesa ya daka masa tsawa, sannan ya umarci askarawansa su yi waje da shi.
Aka yi taro lafiya aka gama. Ashe bawan nan na Sarki ya yi matuƙar kufula da cin mutumcin da Attajiri ya yi masa, duk da shi ma ya san ya yi kuskure. A ranar da abin ya faru ma, bai iya bacci ba. Yana ta ƙulla Makircin da zai yi don ɗaukar fansa akan attajiri.
Sai bawan ya fara rayawa a ransa "Idan da zan san hanyar da zan bi don Sarki ya wulaƙanta Tajirin nan, da na ɗauki fansa ta. To amma ta yaya ƙasƙantaccen mutum iri na zai iya ɗaukar fansa akan mutum mai daraja irin sa?".
A ƙarshe dai, wata dabara ta faɗo masa a rai.
Bayan wasu 'yan kwanaki, wannan bawan ya shiga ɗakin Sarki shara da sanyin safiya, a lokacin sarki na kan gadonsa yana bacci, amma da alamun baccin da sarki yake yi ba mai nauyi ba ne.
Da bawan nan ya gane haka, sai kuwa ya fara maganganu ƙasa-ƙasa shi kaɗai, yana cewa "Duniya da abin mamaki take, yanzu a ce har Attajirin bafatake ya sami sukunin rungumar matar sarki?..ooo."
Caraf kuwa sai a kunnen sarki. Ya yi firgigit ya farka, da yake mutum ne shi mai kishi. Ya kalli bawan nasa fuskarsa a murtuƙe ya ce " da gaske kake? Ka taɓa ganin attajiri ya rungumi matata?"
Bawa ya ɗuka gaban sarki, ya ce "ya shugabana, kwana biyu ba na samun yin bacci, yanzu ma gyangyaɗi ke ɗiba ta. Idan ka jini na faɗi wata magana da ba ta gamsar da kai ba, ka yafe ni".
Shikenan, Sarki bai sake cewa bawa uffan ba. Sai dai tunane-tunane da suka yawaita zagaya masa a zuciya.
'Wannan bawan nawa ba shi da shamaki a gidan nan, shi ma wannan attajirin haka, wataƙila akwai abin da bawan ya hango yake tsoron faɗa mini'
Daga nan fa sai sarki ya cika da kishi, ya fara yanke alaƙoƙinsa da attajirin nan. Kana ma, ya ce da dakarunsa kada su ƙara barin attajiri ya shigo masa gida.
Duk abin da ake Attajiri bai sani ba, wata rana ya yi niyyar zuwa kawowa Sarki wata kyauta bayan ya dawo daga fataucinsa, da ya zo shiga sai masu jiran ƙofa suka ce sam ba zai shiga ba, suka sanar masa da cewa sarki ya hana su yin haka gare shi.
Wannan abu ya yi matuƙar girgiza attajiri. Sai ya shiga kokwanton dalilin da yasa sarki ya ɗauki wannan hukunci a gare shi.
Ashe bawan sarkin nan yana bisa bene, kuma duk yana hangen abinda ke faruwa. Daga can nesa ya ɗaga murya yana cewa "kai dakaru, wannan Bafatake abin so ne ga sarki, mutum ne mai daraja, zai iya sanyawa a ɗaure mutum ko a sake shi kamar yadda ya sanya aka kore ni a ranar da ake walima a gidansa. Ku kula da kanku, abin da ya same ni na iya samunku"..
Dajin haka, sai wannan attajiri ya gano bakin zaren. Ya ɗaga kansa ya kalle shi, sannan ya yi murmushi. Bai ƙara ce musu uffan ba, ya juya abinsa zuwa gida.
Attajiri ya yi tunanin matakin da ya kamata ya ɗauka. Har wata zuciyar ta shawarce shi da ya haifarwa da sarki matsala a mulkinsa kasancewar shi mutum ne da kowa ke so a garin, amma sai ya tuna da cewa shi matafiyi ne, ya zaga duniya, ya san illar rikici, don haka zaman lafiya ya kamata ya nema ba tashin hankali ba.
Bayan wani lokaci sai ya aika aka kira masa wannan bawa na sarki. Ya yi masa karramawa sosai da kyaututtuka, sannan ya nemi gafarar sa akan abinda ya yi masa a baya.
Wannan abu ya farantawa bawan sarki rai. Har ma yake cewa attajiri "Ranka ya daɗe, na gafarta maka, ka girmamani, ka kuma nemi afuwa ta. Don haka zan yi ƙoƙarin juyo da hankalin sarki gare ka ta yadda za ku ci-gaba da mu'amala kamar yadda kuka saba"
Abinda aka yi kenan, kashe gari da sassafe bawa ya shiga ɗakin sarki shara kamar wadda aka yi kwanakin baya, sai ya hau surutunsa ƙasa-ƙasa yana cewa "a'aha, muna da wawan sarki a garin nan, kalli yadda ya ci kabewa ya zubar a ɗakinsa. Abar da ake miya amma ita yake ci.."
Nan ma dai sarki ya yi wuf ya juyo gare shi, ya ce "kai wanne irin wawa ne, a ina kaga na ci kabewa na watsar a ɗakin nan?"
Bawa ya faɗi gaban sarki yana neman yafiya, ya bada uzurin rashin bacci ne ke sa shi yin gyangyaɗi idan yana aiki kamar yadda ya bayar a baya.
Tun daga nan, sai sarki ya gane ƙarya bawan yake faɗa a duk maganganunsa, sai kuma ya yi da-na-sanin hukuncin da ya ɗauka akan Attajiri ba tare da ya yi bincike ba. Nan take ya sa a kira masa shi don ya nemi afuwar sa, ya kuma yi masa tanajin kyauta gagaruma.
Ƙarshen hikayar kenan.
Darussa:
Kada ka raina mutum duk kaskancinsa.
kada ka kai kanka matsayin da ba naka ba.
Kada ka rinƙa saurin yarda da magana tare da ɗaukar mataki.
Kada ka yi girman kai wajen neman afuwar laifin da ka aikata.