Wednesday, 11 September 2024

Ire-iren Abubuwan Da Shaiɗan Yake Yaudarar Jama'a Da Su

Tura Wannan Zuwa Ga

Alkur'ani mai girma ya bayyana mana wane ne Sheɗan da siffofin sa da ayyukan sa, da makircin sa, da tsananin gabar sa ga musulmi ko mutum ko aljan, domin ya ga ya raba shi da hanyar tsira.


Abubuwan Da Shaiɗan Yake Yaudarar Jama'a Da Su
Hoto: Ebaznica

MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


Kuma zai fitowa mutum ta duk hanyar da ya ga za ta fiye masa sauƙi, zai iya raba mutum da tauhidi ya koma yana shirka, zai iya raba mutum da sunna ya koma yana bidi'a, zai iya raba mutum da nagarta ya koma yana zina ko luwaɗi ko shan giya, ko kisan kai, zai iya raba mutum da kamewa ya koma yana aikata shashanci da sharholiya bayan da mutum ne mai kamewa, zai iya sakawa mutum tsoro da waswasi ko wata shubuha, ko wata sha'awa ko riya, ko san shugabanci ko mugun son kuɗi ta kowacce hanya, ko ya sa wa mutum wani mummunan zato da kokwanto game da Allah ko Annabi ko lahira ko Kur'ani, ko ya sa wa mutum waswasi akan ibada, yana yi yana sakewa, domin yana cewa ta farko ba ta yi ba.


Sheɗan yana iya halakar da kowa Malamai, Shugabanni, masu kuɗi, maza, mata, yara manya, waɗanda ba ya iya halakarwa su ne kawai Annabawa, amma duk wanda ba Annabi ba, Sheɗan zai iya cusa masa wani abu mara kyau, ko ƙarami ko babba,  Annabawa su ne kaɗai ma'asumai (Waɗanda Allah ya tsare, Sheɗan ba ya galaba akan su).

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user