Monday 16 September 2024

Zafafan Gajerun Sakonnin Soyayya A Rubuce

Tura Wannan Zuwa Ga

Zuciya ba ta da ƙashi a kan iya tanƙwarata yadda ake so, amma soyayyarki ba ta canzuwa a zuciyata duk tsananin rayuwa.


Gajerun Sakonnin Soyayya A Rubuce
Hoto: Freepik


Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Zan ba ki duk abin da na mallaka amma ban da raina, idan na ba ki raina ta ya zan yi rayuwa da ke?


Ke ce burina, duk iya ƙwarewata a kan soyayyarki take aiki, saboda ke kaɗai kawai nake so. Murmushinki abin nema ne a gare ni, dariyarki farin ciki ne na musamman.


Ina son ki har abada, ba na buƙatar taimakon kowacce mace idan ba ke ba, naki kawai nake buƙata. Misalin soyayyata shi ne misalin ruwan teku, ba ya taɓa bushewa.


Ban da numfashi ke ce abu na biyu da nake buƙata domin na yi rayuwa. Sarauniyata! Farin ciki kamar wani magani ne da ba ya lalacewa, kuma kowa yana da damar samun shi, misalin ni da ke.


Kin ɗauke makullin shiga zuciyata, don haka babu wata mace da za ta samu damar shiga, ke ce sarauniyar zuciyata.


Ana faɗin Ɗan Adam yana yin gamo, ashe ni da ke na yi gamo ban sani ba, ke ce kawai za ki iya wadatar da ni a duk faɗin duniyar nan, ke rabin jikina ce, kamar yadda ake gane farin fulawa a cikin jajayen furanni, haka soyayyar ki take ba ta ɓoyuwa a zuciyata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user